Yanzun nan: Dole ta sa an garkame Makarantu ganin zanga-zanga ta ki cinyewa
- Zanga-zangar #EndSARS da ake yi ta tursasa rufe Makarantu a Oyo
- Kafin nan gwamnonin Jihohi sun maka dokar ta-baci a Legas da Edo
- Yanzu haka Sanatoci su na zama na musamman a majalisar dattawa
Zanga-zangar da ake ta faman yi a bangarorin Najeriya ya yi dalilin da ya sa aka rufe makarantun kasuwa da na gwamnati a fadin jihar Oyo.
Wannan zanga-zanga da akasari matasa su ke gudanar wa ya jawo cikas wajen harkar karantarwa a Oyo, jim kadan da komawa karatu a kasar.
Jaridar The Nation ta ce an rufe makarantun boko a jihar duk da cewa gwamnati ba ta fitar da takarda ta na umurtar a dauki wannan mataki ba.
KU KARANTA: #IStandWithBuhari za su yi tattakin lumana a Birnin Tarayya
La’akari da yadda aka gaza kawo karshen wannan zanga-zanga bayan fiye da mako guda ya sa iyaye da dalibai su ka kaurace wa makarantu.
Makarantun kasuwa sun aika wa iyayen yara takarda a daren ranar Lahadi, su na bada shawarar a guji kawo yara makaranta saboda halin da ake ciki.
Irinsu yankin Apata, New Garage, 110, Omi Adio, Molete, Beere, Ojoo, Moniya, da titin Ibadan a jihar Oyo ba su shiguwa saboda zanga-zangar da ake yi.
A daidai wannan lokaci kuma majalisa ta kira taron gaggawa na musamman a ranar Talata.
KU KARANTA: #EndSARS Gwamnati ta sa dokar ta baci a Legas
Ana tunanin cewa Sanatoci sun shiga bayan labule a majalisar ne domin kawo karshen wannan zanga-zanga da ta ci bangarorin kasar daban-dabam.
Bude majalisa yau ke da wuya, Ahmad Lawan, ya bukaci ayi zaman gaggawa da karfe 10:55.
A yau aka ji cewa ‘yan zanga-zanga sun jawo aiki ya tsaya cak a Legas da karfi da yaji. Legas da ta saba tatsar kudin bin hanyoyi ta gagara yin hakan a yanzu.
Rufe manyan hanyoyi da kofofin shiga garin da aka yi ya sa jihar ta tafka asarar N230m.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng