Kwankwaso ya bude gidan rediyo a Kano, ya nada Maude Gwadabe shugaba

Kwankwaso ya bude gidan rediyo a Kano, ya nada Maude Gwadabe shugaba

- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jihar Kano ya bude gidan rediyo a Kano

- An bude gidan rediyon mai suna Nasara bayan amincewar NBC da aka samu

- Baya ga haka, Kwankwaso ya nada Dr. Maude Gwadabe a matsayin shugaban gidan rediyon na farko

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban kungiyar Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso, ya kafa gidan rediyo a jihar Kano kuma ya nada tsohon dan jaridar BBC, Maude Gwadabe a matsayin manajan farko.

Gidan rediyon mai suna Nasara Rediyo, ya samun amincewar hukumar yada labarai ta kasa NBC, da su fara watsa labarai a kan 98.5 FM, Daily Nigerian ta wallafa.

A wata takarda da sakataren kwamitin gidan rediyon, Sanusi Dawakin-Tofa ya ce: "An kafa gidan rediyon Nasara ne domin habaka da kare al'umma.

"Akwai jin dadi idan aka samu zakakuran ma'aikata da za su ja ragamar gidan rediyon. Babu shakka Dr. Maude kwararre ne a fannin yada labarai a karni na 21. Ina taya shi murna tare da sauran ma'aikatan."

Dawakin-Tofa ya yi kira ga sauran gidajen rediyon da ke garin Kano da su yi gasa mai kyau tare da kiyaye dukkan dokokin hukumar yada labarai.

KU KARANTA: Filayen sauka da tashin jiragen sama 5 masu matukar kyau a Afrika

Kwankwaso ya bude gidan rediyo a Kano, ya nada Maude Gwadabe shugaba
Kwankwaso ya bude gidan rediyo a Kano, ya nada Maude Gwadabe shugaba. Hoto daga @BBCHausa
Asali: UGC

KU KARANTA: Babur din zinari: Hotunan kasaitattun ababen hawan Shugaba Donald Trump

A wani labari na daban, ministan tsaro, Bashir Magashi, ya ja kunnen matasan Najeriya akan kada su keta iyakar tsaro sakamakon zanga-zangar rushe SARS duk da gwamnatin tarayya ta fahimci manufarsu.

Magashi yayi wannan kiran ga matasa a wata takarda da kakakin ma'aikatar, Mohammad Abdulkadri ya saki, kamar yadda jaridar Premium times ta ruwaito.

Ma'aikatar ta yi wannan jan kunnen a lokacin da shugaban kamfen din Buhari, Danladi Pasali, ya jagoranci wakilai a ma'aikatar tsaro dake Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel