Yanzu Yanzu: Yan sanda sun harba wa masu zanga-zanga barkonon tsohuwa a Abuja

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun harba wa masu zanga-zanga barkonon tsohuwa a Abuja

- Jami'an rundunar yan sandan Najeriya sun bada wa masu zanga-zanga barkonon tsohuwa a babbar birnin Abuja

- Hakan ya biyo bayan kokarin shiga fadar Villa ta kofar baya da masu zanga-zangar suka yi

- Yan sandan dai sun tare masu zanga-zangar ne a kan Titin John Kennedy

Jami’an yan sanda sun harba barkonon tsohuwa a kan masu zanga-zangar kawo karshen rundunar SARS a Abuja, babbar birnin tarayyar kasar, Channels Tv ta ruwaito.

Jami’an tsaron sun tsare masu zanga-zangar wadanda ke neman a kawo karshen cin kashin da yan sanda ke yi wa mutane a unguwar John Kennedy yayinda suke kokarin shiga fadar Shugaban kasa ta kofar baya.

A kokarinsu na tarwatsa masu zanga-zangar wadanda suka kasance a gidan mulki da ke Asokoro, jami’an yan sanda sun watsa masu barkonon tsohuwa.

KU KARANTA KUMA: Da ɗuminsa: Yan ta'adda sun kaiwa jami'an ƴan sandan RRS hari a Lagos

Da farko dai sojoji sun sanya shingen binciken ababen hawa a hanyar Mararaba/Nyanya wanda ke sada jihar Nasarawa da babbar birnin tarayyar kasar, Abuja.

Hakan ya tursasa wasu fasinjoji tafiya a kafa yayinda wasu masu motar kasuwa suka bar hanyoyi saboda tsoron kada cunkoso ya cika da su yayinda shahararren shataletalen Aya ke cike da jami’an yan sanda da na NSCDC.

Har ila yau, an girke jami’an yan sanda a gaban hedkwatar babban bankin Najeriya (CBN).

KU KARANTA KUMA: Da ɗuminsa: Gwamnatin Edo ta sanya dokar ta ɓaci ta awanni 24 a fadin jihar

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun harba wa masu zanga-zanga barkonon tsohuwa a Abuja
Yanzu Yanzu: Yan sanda sun harba wa masu zanga-zanga barkonon tsohuwa a Abuja Hoto: News Colony
Asali: UGC

A gefe guda, mun ji cewa an fito da dakarun soji zuwa kan titunan Abuja domin shawo kan zanga-zangar ENDSARS da ta fara sauya salo.

Zanga-zangar ENDSARS a Abuja ta fara sauya salo tare da neman rikidewa zuwa rikici sakamakon harin da wasu batagari ke kaiwa ma su zanga-zangar.

Batagari a Abuja na kai hari kan ma su zanga-zangar nuna adawa da rundunar SARS da kuma ma su zanga-zangar nuna goyon bayan rundunar SARS.

Lamarin, a yawancin lokuta, ya haddasa gumurzu tare da zama sanadiyyar raunata mutane da kuma lalata dukiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel