Ruth Inomina: Mutumiyar Neja-Delta ta samu shiga Sojan ruwan USMV
- Ruth Inomina ta shiga sahun mutanen da su ka yi wa Najeriya abin alfahari
- Inomina ainihin ‘Yar yankin Neja-Delta ta ce da ta zama soja a kasar Amurka
- Yanzu wannan budurwa ta na cikin sojojin saman kasa mai karfi a Duniya
A lokacin da wasu miyagun su ke jawowa Najeriya bakin-jini a kasashen waje, Ruth Inomina ta yi abin kirki, inda ta zama abin alfaharin asalin ta.
Miss Ruth Inomina ta zama soja a Amurka, kasar da ta fi kowace karfin iko a fadin Duniya.
An kaddamar da wannan Baiwar Allah a matsayin sojan ruwan. Ruth Inomina ta fito da mukamin Second Lieutenant a gidan soja na kasar ta Amurka.
KU KARANTA: 'Dan Najeriya da ya je ci rani a Amurka ya na neman zama Gwamna
Ainihin wannan Budurwa dai mutumiyar yankin Neja-Delta ce da ke bangaren kudu maso kudancin Najeriya, a yankin da ake da arzikin man fetur.
Wani Bawan Allah mai suna Justice O. Derefaka, ya bada sanarwar wannan labari na Inomina. Derefaka ya bayyana wannan ne a shafinsa na LinkedIn.
Justice O. Derefaka ya yi kira ga jama’a, musamman mutanen Najeriya da ke kasashen ketare, su taya wannan Budurwa nasarar matsayin da ta samu.
KU KARANTA: Jami'an Amurka sun kama Invictus Obi a filin jirgin sama
Rahotanni sun tabbatar da cewa jami’an sojin kasar Amurka su na tashi da albashi kimanin $20000 zuwa $50000 duk wata, kusan Naira miliyan 10.
A ‘yan kwanakin bayan nan, an samu wasu asalin ‘yan Najeriya da Afrika da su ka jawowa nahiyar a yaba, daga ciki har da irinsu Kelechi Madu.
Idan za ku tuna, wani ainihin 'Dan Najeriya mai suna Mista Kelechi Madu ya zama Minista a gwamnatin kasar Kanada a watan Agustan 2020.
Yanzu haka Kelechi Madu ya zama ministan shari'a kuma babban Lauyan Alberta a Kanada.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng