Jihar Bayelsa ta jinjina wa Gwamnatin Buhari kan biyan Jihohi kudin aiki
- Gwamnati ta na maida wa Jihohin abin da su ka kashe wajen aikin tarayya
- Gwamnan jihar Bayelsa ya ji dadin wannan kokari na shugaban kasa Buhari
- Hakan ya sa ya fito ya jinjinawa gwamnatin APC da ya gana da 'Yan Majalisa
Gwamnatin jihar Bayelsa ta yaba da kokarin Muhammadu Buhari na dawo wa jihohi kudinsu da su ka kashe wajen ayyukan gwamnatin tarayya.
Gwamnan na Bayelsa ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne lokacin da zauna da ‘yan kwamitin harkar bashi na majalisar tarayya jiya.
Hukumar NAN ta fitar da rahoto cewa gwamna Douye Diri ya yi wata ganawa da Sanatoci da ‘yan majalisar wakilan tarayya a babban birnin Yenagoa.
KU KARANTA: An ambaci Gwamnonin da ya kamata su zauna da Buhari kan yajin-aikin ASUU
Mataimakin gwamna, Lawrence Ewhrudjakpo ne ya wakilci mai girma gwamna a wannan zama.
Gwamna ta bakin Sanata Lawrence Ewhrudjakpo ya ke cewa abin da gwamnatin tarayya ta yi zai taimaka wa jihohi wajen gina abubuwan more rayuwa.
Jawabin ya fito ne ta bakin mai taimakawa Lawrence Ewhrudjakpo wajen yada labarai, Mista Doubara Atasi a ranar Lahadi, 18 ga watan Oktoba.
Ewhrudjakpo ya ji dadin ziyarar da ‘yan majalisar su ka kawo, ya ce babu yadda za a iya gudanar da gwamnati ba tare da sa hannun ‘yan majalisa ba.
KU KARANTA: ASUU: Matasa sun ce Gwamnonin Borno da Zamfara su zauna da Buhari
“Majalisar tarayya ta na da muhimmanci sosai, amma ba a damuwa da ita a kasar nan saboda su ne sababbin shiga harkar gwamnati.” Inji Ewhrudjakpo.
“Amma ka da su manta, idan babu doka, babu dubiya da wakilci, to ba za a samu damukaradiyya ba. A kan wadannan ne aka kafa mulkin farar hula.”
Sanata Clifford Odia da Hon. Dayyabu Saffana sun zo ne domin tabbatar da ayyukan da ake yi.
Dazu nan ku ka ji cewa Gwamna Dave Umahi zai tattara da shugabannin kananan hukumomin Ebonyi su koma jam'iyyar APC daga PDP mai hamayya.
Wasu su na ganin Gwamna Dave Umahi zai sauya-sheka ne saboda ya nemi babbar kujera a 2023.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng