COVID-19: Sabbin mutane 133 sun kamu da Korona, mutane 2 sun mutu nan take

COVID-19: Sabbin mutane 133 sun kamu da Korona, mutane 2 sun mutu nan take

- Hukumar NCDC ta bayyana cewa karin mutum biyu sun mutu sakamakon cutar korona a Najeriya

- Har ila yau, karin mutum 133 sun kamu da cutar a jihohi tara

- An kuma sallami mutum 54 daga cibiyar killace wadanda suka harbu bayan sun warke

Hukumar kula da hana yaduwar cututtuka a Najeriya (NCDC) ta sanar da cewar sabbin mutane 133 sun kamu da cutar korona a cikin kasar.

NCDC ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter a ranar Lahadi, 18 ga watan Oktoba.

Kasar ta kuma samu karin mutum biyu da cutar ta kashe, a yanzu jumillar wadanda suka mutu sakamakon harbuwa da ccutar sun kai 1,125.

Cibiyar ta kuma bayyana cewa an sallami marasa lafiya 54 daga cibiyar killace wadanda suka harbu a fadin kasar.

COVID-19: Sabbin mutane 133 sun kamu da Korona, mutane 2 sun mutu nan take
COVID-19: Sabbin mutane 133 sun kamu da Korona, mutane 2 sun mutu nan take Hoto: @NCDCgov
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Wacce ta tsira a hatsari jirgi: Hotunan zazzafar shigar da Kechi Okwuchi ta yi

Ta bayyana cewa karin mutum 133 da suka kamu da cutar sun kasance a jihohi tara da suka hada da Legas, wadda ke kan gaba da mutum 90, sai Rivers mai 13 da kuma Kaduna da Abuja masu 8-8 kowaccensu.

A cewar hukumar, tun bayan barkewar annobar a Najeriya a cikin watan Fabrairu, NCDC ta yi wa mutane fiye da 578,841 gwaji, inda daga cikinsu mutum 54,587 suka nuna suna dauke da ita.

Jumillar wadanda annobar cutar korona ta kama a Najeriya sun zama 61,440, sannan kuma an sallami mutum 56,611 bayan sun warke.

KU KARANTA KUMA: Dakarun sojoji sun yi artabu da yan bindiga a Filato, sun kashe mutum daya

Kun ji cewa cewa dalibai da malaman wata makaranta mai zaman kanta dake unguwar Lekki, a jihar Legas sun kamu da mugun cutar Korona.

Legit.ng ta tattaro cewa kwamishanan lafiyan Legas, Akin Abayomi, ya ce an gano sun kamu da cutar ne bayan binciken da aka gudanar a makarantar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel