Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari na ganawar sirri tare da Lawan da Gbajabiamila

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari na ganawar sirri tare da Lawan da Gbajabiamila

- Shugaban kasa Buhari na ganawar sirri tare da shugabannin majalisar dokokin tarayya

- Bashir Ahmad, mai ba Shugaban kasa shawara na musamman a shafukan zumunta ne ya tabbatar da ci gaban a wani wallafa da ya yi a Twitter

- Ana sa ran Shugaban kasar da shugabannin majalisar za su tattauna ne kan zanga-zangar da ke gudana na neman a kawo karshen SARS

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugabannin majalisar dokokin tarayya na cikin wata ganawar sirri a yanzu haka.

Hadimin Shugaban kasa Buhari na musamman a shafukan zumuntar zamani, Bashir Ahmad ne ya tabbatar da hakan a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter, @BashirAhmaad a ranar Lahadi, 18 ga watan Oktoba.

A cewar Ahmad, Shugaban kasar na ganawa da Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila kan zanga-zangar da ke gudana.

Taron na zuwa ne kan gangamin gama gari da ake yi kan cin zarafin da yan sanda ke yi a Najeriya.

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari na ganawar sirri tare da Lawan da Gbajabiamila
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari na ganawar sirri tare da Lawan da Gbajabiamila Hoto: @GuardianNigeria
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Daga karshe Oyetola ya yi martani kan harin da aka kai masa, ya ce an turo yan daban ne domin su kashe shi

A tuna cewa kungiyar gwamnonin Najeriya ta sanya baki a zanga-zangar da ke gudana a fadin kasar kan rundunar yan sanda.

Gwamnonin sun gana da Sufeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu a ranar Asabar, 14 ga watan Oktoba a Abuja kan lamarin da kuma mafita yayinda zanga-zangar ke dada yaduwa a yankunan kasar.

Gwamnonin sun kuma yanke shawarar ganawa da shugabannin zanga-zangar domin tausarsu a kan kawo karshen gangamin.

KU KARANTA KUMA: Lawan ya dauki nauyin aurar da marayu da marasa gata su 100 a Yobe

A wani labarin, uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari, a ranar Asabar, 17 ga Oktoba, ta daura wani gajeren sako amma mai dauke da ma'anoni da yawa a shafinta na Tuwita @aishambuhari.

Sakon da ta daura na cewa #Achechijamaa, bata fito karara ta yi bayani ba, amma ta daura sakon tare da hoton mijinta, shugaba Muhammadu Buhari yana zaune da hafsoshin tsaro.

Hakazalika ta hada maganan da waka mai bukatar dauki na ceton Arewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel