‘Yan bindiga sun harbe wani Malamin Jami’ar Kebbi, Abdullahi Dakingari

‘Yan bindiga sun harbe wani Malamin Jami’ar Kebbi, Abdullahi Dakingari

- Wani malami a Jami’ar tarayya da ke Birnin Kebbi ya rasu a makon nan

- An hallaka Malam Abdullahi Abubakar Dakingari ne a birnin tarayya Abuja

- Har yanzu ba a san wadanda su ka kashe wannan mutum mai shekara 38 ba

Wasu miyagun ‘yan bindiga da ba a sansu ba, sun hallaka wani malamin makaranta a jami’ar tarayya da ke Birnin Kebbi, jihar Kebbi.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ‘yan bindiga dadi sun harbe Malam Abdullahi Abubakar Dakingari, wannan ya faru ne a birnin Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa an bindige Abdullahi Abubakar Dakingari ne a lokacin da ya zo duba mahaifinsa da ke jinyar rashin lafiya a asibiti.

KU KARANTA: Shugaban kasa ya aika wa Gwamnan Jihar Oyo sakon ta’aziyya

Wannan mummunan lamarin dai ya auku ne a lokacin da ake kukan rashin tsaro a fadin Najeriya.

Kamar yadda jaridar ta bayyana, an kashe Marigayi Abdullahi Abubakar Dakingari ne a unguwar Life Camp lokacin da harbe-harbe ya barke a yankin.

‘Danuwan mamacin, Abubakar Mu’azu Dakingari ya tabbatar da rasuwarsa a lokacin da ‘yan jarida su ka tuntube shi a cikin karshen wannan makon.

KU KARANTA: An kama ganduroba da tabar wiwi

‘Yan bindiga sun harbe wani Malamin Jami’ar Kebbi, Abdullahi Dakingari
Jami'ar Birnin Kebbi Hoto: myschool.ng
Asali: UGC

Malam Abubakar Mu’azu Dakingari ya shaidawa manema labarai cewa malamin makarantar ya mutu ya bar matar da za ta masa takaba da kuma ‘diya.

Wani Bawan Allah da ya san marigayin mai shekara 38 ya ce ya san shi a mutumin kirki.

A makon nan ne kuma mu ka ji cewa Gwamnatin tarayya ta dauki matakin tabbatar da tsaron jirgin Abuja – Kaduna ta hanyar kafa wasu na'urori.

Gwamnati za ta kashe N1.28bn wajen wannan aiki kamar yadda Rotimi Amaechi ya bayyana.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel