FEC ta amince da sayen kayan tsaron N1.28bn a jirgin kasan Abuja zuwa Kano

FEC ta amince da sayen kayan tsaron N1.28bn a jirgin kasan Abuja zuwa Kano

- FEC ta amince da bada aikin sayen kayan tsaro a tashar jirgin Abuja zuwa Kano

- Ana kukan tsageru su na kai hare-hare a wasu tashoshin jirgin kasan na Kaduna

- Ministan sufuri ya ce gwamnati za ta kashe N1.28bn domin kara samar da tsaro

Majalisar zartarwa ta yi na’am da kashe Naira biliyan 1.28 domin sayen na’urorin tsaro da za a kafa a tashoshin jirgin kasan Abuja-Kaduna-Kano.

Hukumar NAN ta ce gwamnatin tarayya ta cin ma wannan matsaya ne a taron mako-mako na FEC wanda aka yi a ranar Larabar nan, 14 ga watan Oktoba.

Ministan sufuri na kasa, Rotimi Amaechi, ya bayyana haka a lokacin da ya yi magana da ‘yan jarida bayan an kammala taron FEC na makon nan.

KU KARANTA: Masu zanga-zangar #EndSARS sun sa an kashe Direban Minista

A cikin ‘yan kwanakin nan, an rika samun hare-hare a tashar jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

“Mun gabatar da takarda a kan kawo kayan tsaro, tare da sauke wa da kafa su, da gwaji da kuma kaddamar da su a tashohin jirgin kasa bakwai a kasar nan.”

Rotimi Amaechi ya ce tashoshin jirgin su ne: Idu, Rigasa, Jere, Kubwa, Kaduna da kuma Kano.

Ministan tarayyan ya ce za ayi duk wannan ayyuka ne a kan N1, 208, 325,464.60, hade da kudin haraji na 7.5%. Za a dauki shekara daya ana wannan aiki.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta zauna da ASUU a kan yajin-aiki

FEC ta amince da sayen kayan tsaron N1.28bn a jirgin kasan Abuja zuwa Kano
Taron FEC Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Amaechi ya yi wa ‘yan jarida bayani game da sakamakon taron na su ne tare da takwarorinsa; Isah Pantami; Saleh Mamman, da shugaban BPE, A. Mamman.

A jiya kun ji Ministan yada labarai, Lai Mohammed, ya yi magana a madadin Babatunde Fashola, ya ce an amince da aikin titin Apapa-Oworonsoki-Ojota a Legas.

Alhaji Lai Mohammed ya ce kamfanin Dangote zai aikin ne a maimakon biyan gwamnati haraji.

Bayan haka majalisar zartarwar ta amince da karin Naira bilyan 8 a kan kudin gyaran titin da ya wuce ta wudil da ke jihar Kano har zuwa garin Maiduguri.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel