COVID-19: Gwamnati za ta rabawa Manoman Jihar Katsina kayan noma

COVID-19: Gwamnati za ta rabawa Manoman Jihar Katsina kayan noma

- Za a tallafawa Manoma a Katsina da iri, takin zamani da ma kayan aiki

- Manoman Katsina za su samu tallafi musamman wajen noman alkama

- Gwamnati za ta kuma raba na’urori kyauta saboda radadin Coronavirus

Akalla kananan manoma 150, 000 za su amfana a jihar Katsina daga tallafin gwamnatin tarayya na rage radadin annobar COVID-19.

Wani babban jami’in gwamnatin tarayya ya bayyana haka a ranar Laraba, 14 ga watan Oktoba.

Darektan ma’aikatan harkar noma da cigaban karkara a ofishin jihar Katsina, Muhammad Salisu-Sule, ya bada wannan sanarwa a jiya.

KU KARANTA: Ministar kudi ta ce an warewa harkar noma N121bn a shekarar 2021

Salisu-Sule ya ce wadanda za su amfana da wannan tallafi za su samu kyautar takin zamani, iri, da kayan feshi da kuma na’urorin ban ruwa.

Jami’in ya ce gwamnatin tarayya za ta raba wadannan kayan gona ne domin rage radadin da annobar COVID-19 ta jefa manoman Katsina.

A cewar Salisu-Sule, har an yi wa duk wadanda za su amfana da wannan tallafi rajista a yanar gizo, kuma za a fara rabon kayan kwanan nan.

NNN ta rahoto wannan jami’in aikin gona ya na cewa za a raba buhuna 450 na nagartattun iri ga manoman jihar domin su noma alkama.

KU KARANTA: Wanene sabon Ministan aikin gona a gwamnatin Buhari?

COVID-19: Gwamnati za ta rabawa Manoman Jihar Katsina kayan noma
Sabo Nanono Hoto: Twitter/NanonoSabo
Asali: Twitter

Malam Salisu-Sule ya ce kayan noman da za a raba, za su bi ta karkashin kungiyar manoman jihar.

Bayan haka, gwamnatin tarayya ta gina hanyoyi a yankunan Zango, Daura, Mai’adua, Funtua and Dandume domin jigilar kayan amfanin gona.

A makon nan ne Ministan noma, Sabo Nanono ya bayyana cewa gwamnatin Nigeria za ta haramta shigo da madara daga shekarar 2022.

Ministan noman ya ce su na kokarin samar da hanyoyin sarrafa madarar da ake da ita a gida.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel