Ma’aikata ta ce shugabanin Kungiyar ASUU da Gwamnati za su sake haduwa yau

Ma’aikata ta ce shugabanin Kungiyar ASUU da Gwamnati za su sake haduwa yau

- An jima ne shugabannin ASUU za ta hadu da wakilan gwamnatin tarayya

- Gwamnatin tarayya ta na rikici ne da malaman jami’a a kan tsarin IPPIS

- Ana sa ran nemo bakin zaren kawo karshen yajin-aikin da ake yi a jami’a

Kungiyar malaman jami’a a Najeriya, ASUU, ta shirya ganawa da bangaren gwamnatin tarayya a yau Alhamis, 15 ga watan Oktoba, 2020.

Wakilan gwamnatin tarayya za su zauna da shugabannin kungiyar malaman makarantar ne a game da yajin-aikin da ake yi a jami’o’in kasar.

Mai magana a madadin ma’aikatar kwadago da samar aikin yi na kasa, Charles Akpan, ya bada sanarwar wannan zama da za ayi a yau.

KU KARANTA: Minista ya bayyana matakan amincewa da bukatun kungiyar ASUU

Mista Charles Akpan ya shaidawa jaridar Daily Trust ta sakon waya cewa gwamnati za ta gana da kungiyar ASUU a yau da karfe 2:00 na rana.

Ko da gwamnati ba ta bayyana dalilin wannan zama ba, ana kyautata zaton cewa makasudin ganawar ba za ta yi nisa da lamarin IPPIS ba.

“Ministan kwadago, Chris Ngige, zai gana da ‘yan kungiyar Malaman jami’a. Za ayi taron ne a ranar Alhamis, 15 ga watan Oktoba.” Inji Akpan.

Tun tuni ake ta samun sabani tsakanin malaman jami’a da gwamnatin tarayya a game da manhajar IPPIS da aka kawo domin biyan albashi.

KU KARANTA: Karin albashin da Buhari ya yi wa Malamai zai jawo matsala - Wike

Ma’aikata ta ce shugabanin Kungiyar ASUU da Gwamnati za su sake haduwa yau
Gwamnati da 'Yan Kungiyar ASUU Hoto: Dailytrust.com
Asali: Twitter

Kungiyar ASUU ta tafi yajin-aiki tun watanni kusan bakwai da su ka wuce, ta na korafin IPPIS bai dace da tsarin aikin malaman jami’a ba.

Kwanaki kun ji cewa gwamnati ta fara duba yiwuwar aiki da manhajar UTAS da ASUU ta kawo a rika biyanta albashi, a madadin IPPIS.

A farkon makon nan ne wakilan kungiyar malaman jami’ar su ka zauna da shugabannin majalisar dattawa a birnin tarayya Abuja.

Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya jagoranci tawagarsa zuwa majalisa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel