Abun mamaki: Saurayi ya nemi auren budurwa a taron zanga zangar EndSARS, ta amince
- Wani dan Najeriya, Demola, a ranar Talata, 13 ga watan Oktoba, ya nemi auran masoyiyarsa a filin zanga-zangar neman a kawo karshen cin kashin da yan sanda ke yi wa jama’a
- Demola ya bayyana cewa abokansa sun kasance a wajen domin mara masa baya yayinda ya dauki wannan mataki na neman auren budurwar tasa
- Mutane da dama na ta yi wa masoyan fatan alkhairi da rayuwa mai albarka a gaba
Zanga-zangar neman a kawo karshen rundunar SARS ya dauki sabon salo a ranar Talata, 13 ga watan Oktoba, lokacin da wani matashi mai suna Demola ya nemi auran budurwarsa a wajen taron.
Idan za ku tuna dai ana gudanar da zanga-zanga a fadin kasar kan neman a soke rundunar SARS sakamakon zarginsu da ake yi da cin zarafin al’umma.

Asali: Twitter
Abunda ya ja hankali game da masoyan shine kasancewar mutane dauke da kwaleyen sanarwar baikon nasu a kewaye da wajen.
KU KARANTA KUMA: EndSARS: Babu bukatar cigaba da zanga-zanga don kun samu abinda kuke so
A kusa da masoyan, an gano wani mai zanga-zanga wanda ya kasance abokin saurayin rike da kwali da aka rubuta: “macen da ta bi ni wajen zanga-zanga za mu nema da aure.”
Matashin saurayin ya tsuguna a kan gwiwarsa yayinda ya gabatarwa da budurwar zoben alkawarin aure.
A cikin daya daga hotunan da ya wallafa a shafinsa na Twitter, an gano masoyiyar tasa tana murna da nuna zoben nata, wanda hakan ke nufin ta amince da shi a matsayin miji.
Kalli hotunansu a kasa:
KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Nigeria za ta haramta shigo da madara daga 2022 - Ministan noma
A wani labarin kuma, 'Yan daban dake dauke da adduna sun kai wa masu zanga-zangar farmaki a daidai Berger, bayan kusan awa daya da fara zanga-zangar.
Sun ci mutuncin masu zanga-zangar har da masu wucewa, inda suka lalata ababen hawan dake wurin.
Sun lalata akalla motoci 5 take anan, sannan sun ji wa masu zanga-zangar munanan raunuka.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng