Ayyukan da gwamnati za ta yi da N3.85tr a shekarar badi – Zainab Ahmed

Ayyukan da gwamnati za ta yi da N3.85tr a shekarar badi – Zainab Ahmed

- Gwamnatin tarayya ta yi maganar yadda za a batar da kudin ayyuka a 2021

- Ministar tattalin arziki ta bayyana abin da aka ware wa ma’aikatun Najeriya

- Ma’aikatar gidaje da ayyuka, lafiya, da tsaro za su samu makudan kudi a badi

Kasafin kudi ya nuna gwamnatin tarayya ta na shirin kashe Naira tiriliyan 3.85 wajen ayyukan more rayuwa a shekara mai zuwa na 2021.

Jaridar Vanguard ta ce wadannan makudan kudi da aka ware domin ayyuka, sun zarce abin da aka yi kasafi a shekarar nan, Naira tiriliyan 2.69.

29% na kasafin kudi badi zai tafi ne wajen manyan ayyuka, gwamnatin Najeriya ta ce ta kama hanyar ware wa ayyuka 30% na kasafin kudi.

Ministar tattalin arzikin kudi da kasafi, Zainab Ahmed, ta bayyana wannan a jiya ranar Talata.

KU KARANTA: Babu sabon abu a cikin kasafin kudin da Shugaba Buhari ya gabatar

Zainab Ahmed ta ce zuwa watan jiya, gwamnatin shugaba Buhari ta fitar da Naira tiriliyan 1.2 daga cikin kudin ayyuka na shekara mai-ci.

Ahmed ta ce gwamnati za ta maida hankali ne a kan kammala ayyukan da aka riga aka fara, a maimakon kinkimo wasu sababbin kwangiloli.

Kamar yadda Ministar ta yi bayani, an ware wa ma’aikatar gidaje da ayyuka Biliyan 404.64, sai kuma ma’aikatar kudi ta samu Biliyan 382.63.

Misis Zainab Ahmed ta ce ma’aikatar sufuri za ta samu Biliyan 256.09 a 2021, daga nan kuma sai ma’aikatar wuta da aka yi kasafin Biliyan 198.2.

KU KARANTA: Minista ya bayyana matakan amincewa da bukatun kungiyar ASUU

Ayyukan da gwamnati za ta yi da N3.85tr a shekarar badi – Zainab Ahmed
Zainab Ahmed Hoto: Thisdaylive.com
Asali: UGC

Ma’aikatar ilmi za ta samu Biliyan 197.41 domin yin ayyukan more rayuwa. Sauran ma’aikatun da ke gaba-gaba su ne na kiwon lafiya da tsaro.

Ministocin harkar ruwa da na kiwon lafiya duk za su samu Biliyan 152.77. Biliyan 121.2 da 110.2 aka ware wa ma’aikatar aikin gona da ta tsaro.

Wata ma’aikata da za ta samu kudi sosai ita ce ta jiragen sama, da aka yi wa kasafin Biliyan 89.

Dazu aka ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala shirin rushe hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC da takwararta ICPC.

Sabuwar hukumar da za a kafa za ta yi aikin da wadannan ma'aikatu da za a rushe su ke yi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel