Austin Chenge zai yi takarar Gwamna a jihar Michigan a Amurka inji NiDCOM
- An samu matashin Najeriya da zai fito neman Gwamna a kasar Amurka
- Austin Chenge zai yi takarar fitar da gwani a karkashin jam’iyyar adawa
- Jam’iyyar Republican za ta yi kokarin karbe mulkin jihar Michigan a 2022
Wani mutumin Najeriya mai suna Austin Chenge ya na cikin wadanda za su nemi yin takarar gwamna a zaben jihohi da za a yi a kasar Amurka.
Austin Chenge zai nemi takarar gwamna ne a zaben 2022 kamar yadda hukumar da ke kula da ‘yan Najeriya da ke gudun hijira, ta bayyana a jiya.
Hukumar dillacin labarai ta ce shugaban yada labarai da hulda da jama’a na hukumar NiDCOM, Abdul-Rahman Balogun, ya bada wannan sanarwa.
KU KARANTA: Donald Trump ya tsure bayan ya kamu da COVID-19
Mista Austin Chenge, wanda ainihinsa mutumin jihar Benuwai ne a yankin Arewa maso tsakiyar Najeriy, ya na harin tikitin takarar gwamna a Michigan
Chenge zai kalubalanci Lamar Smith wanda yanzu haka ya ke majalisar wakilai, wajen samun tikitin jam’iyyar Republican da ta ke adawa a jihar.
Mista Chenge mai shekara 34 da haihuwa ya bayyana burinsa ne tun a watan Maris na bana. Shi ne ‘dan siyasar farko da ya fara bayyana aniyarsa a fili.
NiDCOM ta ce “Chenge ya karanci ilmin shari’a ne a jami’ar Birmingham, kasar Ingila. Tun 2018, ya ke aiki a da sojojin kasar Amurka a matsayin kwararre.”
KU KARANTA: Kiristoci sun bada gudumuwar gina Jami’ar Musulunci a Jigawa
Jawabin ya ce: “An ba shi lambar yabo a dalilin kammala jami’a da ya yi da makin CGPA 99.98%, da kuma irin namijin kokarin da ya ke yi a bakin aiki.”
Daga cikin kokarin da wannan mutumi ya yi a kasarsa Najeriya, shi ne kirkiro wani abin hawa mai kafafu uku wanda ake amfani da shi a kasashen Afrika.
Ku na da labari cewa yanzu haka Gretchen Esther Whitmer ce gwamnan Michigan, har an samu wasu da ke kokarin hambarar da ita daga kan mulki kwanaki
FBI ta ce Gwamnar Michigan, Whitmer ta na cikin wadanda miyagu ke nufin kai wa hari.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng