Majalisa: Kasafin kudin shekarar 2021 ba zai je ko ina ba inji Sanatan hamayya

Majalisa: Kasafin kudin shekarar 2021 ba zai je ko ina ba inji Sanatan hamayya

- Majalisar Dattawa ta fara zama a kan kasafin kudin shekara mai zuwa

- Sanatocin jamiyyar adawa sun soki kundin kasafin kudin da aka kawo

- Wasu ‘Yan Majalisa su na ganin bashin da Najeriya za ta ci ya na yawa

Enyinnaya Abaribe, shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, ya ce kasafin kudin shekarar 2021 da gwamnatin tarayya ta yi ba mai bullewa ba ne.

Sanata Enyinnaya Abaribe ya yi kaca-kaca da kasafin na shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya ce an yi hasashen wasu alkaluma a kan iska da bogi.

Jaridar Premium Times ta rahoto Abaribe ya na kiran kundin kasafin Najeriyar da tsohon labari.

“Kasafin kudin nan ba komai ba ne illa abin da aka saba. Mu na da kasafi kan lissafin da ba zai kai ga ci ba. Ba mu kuma tabbata da yadda halin mai zai kasance ba.”

KU KARANTA: ‘Yar Majalisar Tarayya ta na so a halatta amfani da wiwi

Idan an yi dogaro da hasashe ne a kasafin, na yarda, amma mai zai hana ayi hasashen da kyau.” Inji Sanatan na jam’iyyar PDP.

Ya ce: “Ina so in kara da cewa (kasafin) bai bayyana ainihin kalubalen da mu ke ciki a yau ba.”

A cewar Sanata Abaribe, har yau babu wani sabon labari a kasafin kudin kasar. Sauran Sanatoci sun tofa albarkacin bakinsu a zaman da aka yi a ranar Talata.

Sanatan Ribas, George Sekibo, ya koka ganin kudin da aka ware domin ayyuka bai kai gibin da za a samu a kasafin kudin shekarar mai zuwa ba.

KU KARANTA: Buhari da Osinbajo za su kashe N3.2b a zirga-zirga

Majalisa: Kasafin kudin shekarar 2021 ba zai je ko ina ba inji Sanatan hamayya
Gabatar da kasafin kudin 2021 Hoto: Twitter.com/BashirAhmaad
Asali: Twitter

“Kasafin tiriliyan 13.08 ya na da gibin tiriliyan 5.2. Ta ya kudin ayyuka zai yi kasa da cikon da za ayi. Ina fatan idan aka samu kudin, za ayi abin da ya kamata.”

Ike Ekweremadu ya ce kason bashi da GDP ya haura 3%. Ya ce: “Wannan ne karon farko da za a samu wannan, ina so kwamitin kudi su duba lamarin nan.”

Ekweremadu kamar Atiku Abubakar, ya ja hankali a kan yawan bashin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta ke karbowa, musamman daga kasar Sin.

Idan za ku tuna, shi dai Atiku Abubakar ya na ganin kundin kasafin kudin da Shugaban kasa ya gabatar ya saba dokar kasa saboda adadin bashin da za a karbo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel