Yan bindiga sun kashe mutum 8, sun jikkata wasu uku a Katsina

Yan bindiga sun kashe mutum 8, sun jikkata wasu uku a Katsina

- Yan bindiga sun kai hari wasu kauyuka uku a karamar hukumar Faskari, a jihar Katsina

- A yayin harin, mayakan sun halaka mutane takwas tare da jikkata wasu uku

- Rundunar ya sandan jihar Katsina ta tabbatar da afkuwar al'amari

Wasu da ake zaton yan bindiga ne sun kai farmaki kauyuka uku a karamar hukumaar Faskari da ke jihar Katsina, sun kashe mutum takwas da raunata uku.

Garuruwan da lamarin ya shafa sune kauyen Shau inda a cikinta aka kashe mutum hudu ciki harda wani limami da mataimakinsa; kauyen Ruwan Godiya inda aka kashe mutum biyu sai kuma kauyen Liggel inda aka kashe mutum biyu.

Wani mazaunin yankin ya ce: “Wadannan yan bindiga na zuwa da muggan makamai, wasu irin bindigogi da mutum bai taba gani ba. A kauyen Liggel, wasu garuruwa da ke makwabtaka sun so kawo doki amma yan bindigan su yi wa kauyen zobe ta yadda babu wanda zai iya shiga kauyen ta kowani sako.”

Ya yi zargin cewa a yan kwanakin nan hare-hare ya zama ruwan dare a yakin domin yan bindiga na yawan kai farmaki, har ta kai suna sanar da kauye na gaba da za su kaima hari, cewa “kuma sai sun je sun kaddamar da hari a kauyen.”

Yan bindiga sun kashe mutum 8, sun jikkata wasu uku a Katsina
Yan bindiga sun kashe mutum 8, sun jikkata wasu uku a Katsina Hoto: @PremiumTimesng
Asali: Twitter

Wani kuma ya ce a makon da ya gabata ne yan bindiga suka kashe mutum hudu a kauyen Yankara, biyar a kauyen Yan Tuwaru sannan kuma suka jikkata wasu da dama tare da kona gidajensu da babura.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kungiyar ASUU ta shiga ganawar sirri da shugabannin majalisar dattawa kan IPPIS

Har ila yau sun yi fashin shanaye a kauyen Kamfani, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Mazauna yankin sun yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su kawo masu agaji sannan kuma suka yi kira ga mutane da su taimaka masu da rokon Allah.

Kakakin yan sandan jihar Katsina, SP Isah Gambo, ya tabbatar da lamarin, cewa “a jiya, yan bindiga wadanda ke dauke da muggan makamai sun kai farmaki kauyen Ruwan Godiya sannan suka kashe mutum takwas da kuma jikkata wasu uku.”

“A lokacin da jami’anmu suka isa wajen, yan ta’addan sun tsere, don haka jami’anmu suka kwashi wadanda suka jikkatan zuwa asibiti don jinya,” in ji shi.

Gambo ya yi kira ga tura karin jami’an tsaro, motocin yaki da kuma jirage marasa matuka zuwa jihar domin magance lamarin yadda ya kamata.

KU KARANTA KUMA: Magidanci ya saka wa bishiyarsa raga domin hana makwabta amfana da ita

A wani labarin, Mazauna Pegi, wani gari a yankin karamar hukumar Kuje da ke Abuja, a safiyar ranar Litinin, sun rufe kofar ofishin ministan birnin tarayya.

Sun aikata hakan ne a yayinda suke gudanar da zanga-zangar lumana, jaridar The Nation ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel