Garius Gololo ya na so a goyi bayan Bola Tinubu/Simon Lalong a zaben Shugaban kasa

Garius Gololo ya na so a goyi bayan Bola Tinubu/Simon Lalong a zaben Shugaban kasa

- An fara nuna goyon baya ga takarar Bola Ahmed Tinubu a Arewacin Najeriya

- Daya daga cikin manyan masu wannan kira shi ne jagoran APC, Garus Gololo

- Alhaji Galolo shi ne shugaban kungiyar Makiyaya na Miyetti Allah a Benuwai

Wasu sun fara buga tamburan siyasar 2023, har ta kai ana kira ga tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu ya tsaya takarar shugaban kasa.

Rahotanni sun bayyana cewa ana zuga babban jagoran APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya fara neman kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Masu wannan kira su na so Bola Tinubu ya dauki gwamna Simon Bako Lalong na jihar Filato a matsayin abokin takararsa a jam’iyyar APC mai mulki.

Shugaban kungiyar Makiyaya na Miyetti Allah watau MACBAN na reshen jihar Benuwai, Alhaji Garus Gololo, ya na cikin wadanda ke goyon bayan haka.

KU KARANTA: Mutane miliyan 1 da za su marawa Bola Tinubu baya a zaben 2023

Jaridar Leadership ta fitar da rahoto cewa ya kira taro da ‘yan jarida a garin Abuja, inda ya yi kira ga sauran ‘yan siyasa su hakura da takara, su kyale Tinubu.

Alhaji Garus Gololo ya na so duk masu harin kujerar shugaban kasa su ajiye burinsu a gefe guda, su mara wa tsohon gwamnan Legas da Simon Lalong baya

Gololo wanda jagora ne na kungiyar Makiyayan Najeriya ya na ganin cewa tsohon gwamnan na Legas da gwamna Simon Lalong za su iya doke PDP a 2023.

A na sa ra’ayin, ya na ganin wannan tikiti zai iya ruguza duk shirin da jam’iyyar PDP ta zo da shi.

KU KARANTA: Tinubu da manyan kasa sun samu halartar auren Atiku da Ribadu

Garius Gololo ya na so ayi Bola Tinubu/Simon Lalong a zaben Shugaban kasa
Bola Tinubu Hoto: NaijaNews
Asali: UGC

‘Dan siyasar ya ce shugaba Muhammadu Buhari ba zai zakulo wani ‘dan takara da nufin ya zama magajinsa a 2023 ba, ganin abin da ya faru a zaben Edo.

Ya ce: “Ina kira ga duk wani ‘Dan Arewa da ya ke harin mulki a 2023, ya hakura ya kyale Tinubu, ‘Jagaban na Afrika’, shi ne ya dace ya tsaya takara."

“A tsaida shi takara da Simon Lalong, ba Yakubu Dogara ko kuma Boss Mustapha ba.” Inji sa.

Kwanakin baya kun ji cewa 'Yan Najeriya sun tunawa tsohon gwamnan Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wata magana da ya taba yi a shekarun baya.

A wancan lokaci, Bola Ahmed Tinubu ya fito ya na cewa 'ban yarda da Najeriya ‘kasa daya’ ba.'

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel