Yan bindiga sun halaka mutum biyu wani hari da suka kai garin Bauchi

Yan bindiga sun halaka mutum biyu wani hari da suka kai garin Bauchi

- Yan bindiga sun kai farmaki yankin Gundum Hausawa da ke garin Bauchi

- An tattaro cewa an rasa rayuka biyu a halin wanda aka kaddamar a ranar Lahadi, 11 ga watan Oktoba

- Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da afkuwar lamarin, ta ce an tura jami'an tsaro don daidaita lamura

Hankula sun tashi a yankin Gundum Hausawa da ke garin Bauchi a karshen makon da ya gabata lokacin da yan bindiga suka kai wa al’umman yankin hari.

Akalla mutane biyu aka kashe a harin wanda ya afku a safiyar ranar Lahadi, 11 ga watan Oktoba, jaridar The Nation ta ruwaito.

An tattaro cewa an tsinci gawar mamatan, wani namiji da matashiyar yarinya bayan harin.

Yan bindiga sun halaka mutum biyu wani hari da suka kai garin Bauchi
Yan bindiga sun halaka mutum biyu wani hari da suka kai garin Bauchi Hoto: @TheNationNews
Asali: UGC

Wani mazaunin garin, wanda ya zanta da manema labarai bisa sharadin boye sunansa saboda dalilai na tsaro, ya ce ba a san dalilin da yasa aka kai wa yankin hari ba.

KU KARANTA KUMA: Sunaye da ma'aikatu: Ganduje ya sauya wa manyan sakatarori 8 wurin aiki, ya nada 4 sabbi

Ya roki Gwamna Bala Mohammed da ya gaggauta samar da matakan tsaro a garin.

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar, Ahmed Wakil, ya tabbatar da afkuwar al’amarin, inda ya kara da cewar an fara bincike domin kamo makasan.

Wakil ya ce kwamishinan yan sandan jihar, Lawal Jimeta ya tura jami’an tsaro zuwa yankin domin tabbatar da doka da oda.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su taimakawa yan sanda a bincikensu, ta hanyar bayar da bayanai masu amfani da ka iya kai ga kamun makasan.

KU KARANTA KUMA: 2023: Diyar Atiku Abubakar ta bayyana wanda za ta goyi baya ya shugabanci kasa

Ya bayar da tabbacin cewa zaman lafiya ya dawo yankin yayinda yan sanda ke zuba idanu sosai wajen tsaro.

A wani labari na daban, yan bindiga sun yi garkuwa da mutane da yawa a wani hari da suka kai kan al’umman Kuje, Abuja, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kakakin yan sandan birnin tarayya, ASP Yusuf Mariam, ta tabbatar da faruwar al’amarin a ranar Lahadi, 11 ga watan Oktoba.

Ta bayyana cewa ana nan ana kokarin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel