Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane masu yawan gaske a Abuja

Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane masu yawan gaske a Abuja

- Msu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wasu da dama a harin da suka kai yankin Kuje

- Mai magana da yawun rundunar yan sandan birnin tarayya, ASP Yusuf Mariam, ta tabbatar da faruwar al’amarin

- Lamarin ya afku ne da misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Asabar, 10 ga waatan Oktoba

Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane da yawa a wani hari da suka kai kan al’umman Kuje, Abuja, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kakakin yan sandan birnin tarayya, ASP Yusuf Mariam, ta tabbatar da faruwar al’amarin a ranar Lahadi, 11 ga watan Oktoba.

Ta bayyana cewa ana nan ana kokarin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

An tattaro cewa lamarin ya afku ne da misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Asabar, lokacin da mutanen ke dawowa gida bayan sun je taya sabon sakataren ilimi na hukumar, Mista Yunusa Zakari murna.

Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane masu yawan gaske a Abuja
Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane masu yawan gaske a Abuja Hoto: @PremiumTimesng
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Ministan Buhari da babban basarake sun sha da kyar hannun 'yan daba

Wani tsohon mataimakin Shugaban hukumar, Mohammed Baba da wasu mambobin hukumar na daga cikin wadanda aka sace, kamar yadda rahoto ya kawo.

Yan bindigan sun tsare bas din da mutanen ke ciki sannan suka yi awon gaba da dukkanin mutanen da ke ciki, inda suka keta ta cikin jejin da ke yankin.

Kimanin makoni uku da suka gabata, an kai wani hari makamancin wannan a Tunga Maje da ke Abuja sannan aka sace mutum biyar.

An tattaro cewa an sake su amma babu tabbacin ko jami’an tsaro ne suka ceto su ko kuma an biya kudin fansa ne.

KU KARANTA KUMA: An dakatar da komawa kan sabon tsarin shan wutar lantarki sai wani mako - Minista

A wani labari na daban, an tabbatar da mutuwar mutane 12 sannan mutane 7 sun samu munanan raunuka a wani kauye a jihar Kaduna ranar 11 ga watan Oktoban 2020.

Bayan harin da 'yan bindiga suka kaiwa kauyukan Kidandan da Kadai dake karamar hukumar Giwa dake jihar Kaduna ne aka tabbatar da mutuwar mutane 12 da mutane 7 da suka ji munanan raunuka.

Kamar yadda wadanda suka tsallake rijiya da baya suka tabbatar, wasu 'yan ta'adda da ke tafe da miyagun makamai, sun kaiwa kauyen Kidandan hari a ranar Juma'a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel