Korarren kwamishinan Ganduje ya yi martani a kan dakatar da Dawisu Yakasai

Korarren kwamishinan Ganduje ya yi martani a kan dakatar da Dawisu Yakasai

- Korarren kwamishinan ayyuka da ababen more rayuwa na jihar Kano, Mu'azu Magaji yayi magana akan dakatar da Salisu Tanko Yakasai da Ganduje yayi

- Yace gaskiya bai ji dadin dakatar da mai bada shawara na musamman a harkar yada labarai ba, saboda Salihu amintacce ne ga Gwamna Ganduje

- Magaji ya nuna alhininsa kwarai akan faruwar lamarin, duk da katsalandan din da Yakasai yayi, inda yayi masa addu'o'i da fatan alheri

Korarren kwamishinan ayyuka da ababen more rayuwa na jihar Kano, Mu'azu Magaji yayi magana akan dakatar da Salisu Tanko Yakasai, mai bada shawara na Musamman akan harkokin yada labarai ga Gwamna Ganduje akan shisshigin da yayi ga shugaban kasa.

Magaji ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, inda yace an dakatar da Yakasai.

Korarren kwamishinan Ganduje ya yi martani a kan dakatar da Dawisu Yakasai
Korarren kwamishinan Ganduje ya yi martani a kan dakatar da Dawisu Yakasai. Hoto daga @Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Akeredelu ya lallasa Jegede, ya yi nasara da tazarar kuri'u masu yawa

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa ranar Lahadi, "Gaskiya ban ji dadin dakatar da Salihu Tanko Yakasai da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayi ba.

"Salihu amintacce ne ga Gwamna Ganduje.. Ban ji dadin fitarsa ba. Allah ya zaba masa mafi alkhairi!"

Idan baku manta ba, Gwamna Ganduje ya dakatar da kwamishinan ne sakamakon farin cikin da yayi saboda mutuwar marigayi Abba Kyari, tsohon shugaban ma'aikatan shugaban kasa Muhammadu Buhari, duk da kwamishinan yace ba'a fahimce shi bane.

KU KARANTA: Ku yi rayuwa mai kyau, ko za ku samu makoma kyau - Obasanjo ya shawarci 'yan Najeriya

A wani labari na daban, mai bai wa Gwamna Ganduje shawara na musamman a fannin yada labarai, Salihu Tanko, a ranar Lahadi ya goyi bayan zanga-zangar da ake wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan cin zarafin da 'yan sanda ke yi.

Hadimin ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da rikon sakainar kashi ga muhimman al'amura da suka shafi 'yan Najeriya.

Tanko a wata wallafa da yayi a shafinsa na Twitter da kuma tattaunawa da yayi da jaridar Premium Times, ya ce shugaban kasar ya ci amanar wadanda suka zabesa kuma ya watsa wa magoya bayansa kasa a ido har da shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel