Da ɗuminsa: Ɗan sanda ya shiga sahun zanga zangar ruguza rundunar FSARS

Da ɗuminsa: Ɗan sanda ya shiga sahun zanga zangar ruguza rundunar FSARS

- Wani jami’in dan sandan tafi-da-gidanka ya yi kira ga ruguza rundunar SARS

- Jami’in da ke zanga-zanga ya ce jami’an SARS sun kama dan uwansa

- Yan Najeriya a fadin kasar na kira ga dakatar da rundunar SARS

Wani mutum da aka ce jami’in dan sandan tafi-da-gidanka ne ya shiga sahun masu zanga-zanar neman a ruguza rundunar yan sandan SARS.

Wani bidiyo da ya billo a yanar gizo ya nuno wani mutum sanye da rigar shan iska na rundunar yan sandan Najeriya sannan yana tattaki tare da masu zanga-zangar neman a ruguza sashin yan sandan SARS, jaridar The Cable ta ruwaito.

Da ɗuminsa: Ɗan sanda ya shiga sahun zanga zangar ruguza rundunar FSARS
Da ɗuminsa: Ɗan sanda ya shiga sahun zanga zangar ruguza rundunar FSARS Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa ya biya wasu kudade domin ganin an saki dan uwnsa wanda jami’an SARS suka kama.

Mutumin ya ce:

“Sun kama dan uwana...ni da nake jami’in dan sanda, kun san nawa na biya? Allah ya hukunta su.”

KU KARANTA KUMA: Zaben Ondo: Jerin ƙananan hukumomin da ba'a faɗi sakamakon su ba

KU KARANTA KUMA: Ana fargabar mutum 10 sun mutu, 30 sun jikkata sakamakon hatsarin da treloli biyu suka yi a Adamawa

A baya mun ji cewa fadar shugaban kasa tace an sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari akan zanga-zangar da matasa ke yi saboda kashe-kashen da jami'an SARS ke yi.

Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa akan harkokin watsa labarai ya sanar da hakan a ranar Juma'a, 9 ga watan Oktoba, matasa na tsaka da zanga-zanga akan kisan wulakanci da 'yan sanda ke yi.

Yace Sifeta janar na 'yan sanda, Muhammed Adamu ya sanar da shugaban kasar a ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoba.

Ahmed yace shugaban kasa zai tabbatar ya dauki mataki akai, kuma zai sauyasu da wasu 'yan sandan, yadda zai faranta wa 'yan Najeriya.

Hadimin Buharin ya ce 'yan Najeriya suna da damar bayyanar da damuwarsu idan har shugabanninsu sun yi ba daidai ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel