Gwamnatin Tarayya ta amince ginin titin jirgin kasan Fatakwal - Maiduguri

Gwamnatin Tarayya ta amince ginin titin jirgin kasan Fatakwal - Maiduguri

- Gwamnatin Najeriya za ta gyara titin jirgin kasan Fatakwal zuwa Maiduguri

- Ministan sufuri ya bayyana haka bayan an fito daga taron FEC na makon nan

- Rotimi Amaechi ya nuna Gwamnati a ba za ta kashe kudi sosai wajen aikin ba

Majalisar zartarwa ta FEC ta amince da kwangilar titin dogo daga garin Fatakwal a kudu maso kudancin Najeriya zuwa Maiduguri, jihar Borno.

Gwamnatin tarayya za ta gyara wannan layin dogo, tare da gina sababin hanyoyi da nadaukar kaya.

Jaridar Daily Nigerian ta rahoto Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya na bayyana haka a lokacin da ya zanta da manema labarai a yau ranar Laraba.

Da ya ke zantawa da ‘yan jarida bayan taron Ministocin tarayya a fadar shugaban kasa, Rotimi Amaechi ya ce za a kashe Dala biliyan 3 wajen aikin.

KU KARANTA: ASUU ta dura kan Ministan ilmi bayan ya ce Malamai su koma noma

Bayan haka gwamnatin tarayya ta amince da ginin tashar ruwa a Bonny a karkashin tsarin PPP inda gwamnati da ‘yan kasuwa za su yi karo-karon kudi.

“A yau gwamnatin tarayya ta amince da bada kwangilar gyaran layin dogon Fatakwal zuwa Maiduguri, da sababbin layin daukar kaya.” Inji Amaechi.

Ministan ya ce: “Tirin irgin kasan zai tashi a kan $3,020,279,549. Tashar manyan kayan da za a gina zai tashi a kan $241,154,389.31 a wajen ‘yan kasuwa.”

Tashar cikin ruwan Bonny za ta ci $461,924,369, a nan ma gwamnatin tarayya ba za ta kashe sisi ba.

KU KARANTA: Buhari ya bada hakuri kan dokokin da ya ke kai wa ‘Yan Majalisa

Gwamnatin Tarayya ta amince ginin titin jirgin kasan Fatakwal - Maiduguri
Rotimi Amaechi a Jirgin kasa Hoto: Punch
Asali: UGC

“Titin Fatakwal zuwa Maiduguri zai samu sababbin iyakoki Fatakwal zuwa Bonny, da kuma Fatakwal zuwa Owerri.”

"Za kuma ayi iyakoki a Kafanchan, Gombe ko kuma a yankin Damaturu da Gashua." Kamar yadda Ministan ya yi wa 'yan jarida bayani dazu a garin Abuja.

A yau kuma mu ka ji cewa Farfesa Yemi Osinbajo ya na bayyana cewa Najeriya ta na da miliyoyin jama'a da ke rayuwa cikin tsananin talauci a halin yanzu.

Osinbajo ya fadi hakan ne yayin da ya ke jawabi a wani taro a fadar shugaban kasa a Abuja.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel