Da duminsa: Ƴan bindiga sun kai sabon hari Filato, sun kashe Sarki da mutane huɗu

Da duminsa: Ƴan bindiga sun kai sabon hari Filato, sun kashe Sarki da mutane huɗu

- Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe wani basarase a jihar Filato

- An kuma tattaro cewa sun kashe wasu mutane hudu a harin wanda ya wakana a garin Wereng, karamar hukumar Riyom

- Yan bindigan sun kai hari garin da safiyar ranar Talata, 6 ga watan Oktoba

Wani rahoto daga jaridar The Nation ya nuna cewa yan bindiga sun kashe mutane biyar, ciki harda wani basarake a garin Wereng da ke karamar hukumar Riyom a jihar Filato.

A cewar jaridar, yan bindigan sun kai farmaki kauyen da safiyar yau Talata, 6 ga watan Oktoba, sannan suka fara hari ba kakkautawa, inda hakan ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutum biyar.

Wasu da dama sun ji munanan raunuka.

Da duminsa: Ƴan bindiga sun kai sabon hari Filato, sun kashe Sarki da mutane huɗu
Da duminsa: Ƴan bindiga sun kai sabon hari Filato, sun kashe Sarki da mutane huɗu Hoto: @sblalong
Asali: Twitter

Idan za ku tuna, a baya yan bindiga sun kashe wani basaraken a karamar hukumar Barkin Ladi na jihar Filato, Bulus Janka.

An tattaro cewa an kashe basaraken ne a daren ranar Litinin, 21 ga watan Satumba, a gidansa da ke Rasat, yankin Foron a Filato.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa na ce ba zan yiwa Buhari addu'a ba - Sule Lamido

Istifanus Gyang, wani sanata mai wakiltan jihar Filato, ya byana kisan a matsayin rashin imani.

A martaninsa, gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya ce jami’an tsaro sun kama wadanda suka aikata kisan basaraken da wani jami’in tsaro na farin kaya (DSS).

Ya tabbatar da kama masu laifin a lokacin wata tattaunawa da masu ruwa da tsaki na garin a ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoba.

Lalong ya ba mutanen jihar Filato tabbacin cewa wadanda suka aikata kisan za su fuskanci hukunci.

KU KARANTA KUMA: Ondo 2020: Abdulsalami ya yi kira ga zaben gwamna na gaskiya da lumana

A wani labarin kuma, 'Yan bindiga da ake zargin Fulani ne sun kai hari wasu yankuna biyu da ke karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Kamar yadda Katsina Post ta wallafa, yankunan da aka kai harin sune Tsauwa da Gandu.

Jaridar ta wallafa cewa, a kalla rayuka tara suka salwanta yayin da wasu da yawa suka samu miyagun raunika kuma aka yi garkuwa da wasu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://facebook.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel