Ba ni da makiyan fada – Shugaba Goodluck Jonathan ya fadawa Aminu Shagari

Ba ni da makiyan fada – Shugaba Goodluck Jonathan ya fadawa Aminu Shagari

- Aminu Shehu Shagari ya ce ya gano kuskurensa na kin goyon bayan PDP a 2015

- Ya ce duk abubuwan da Buhari ya fada kan Jonathan da Shagari ba gaskiya ba ne

- ‘Dan siyasar ya roki Jonathan ya yafe masa, kuma tsohon shugaban ya yi afuwar

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce ya karbi rokon da Aminu Shehu Shagari ya ke yi na neman afuwa game da abin da ya faru a 2015.

Dr. Goodluck Jonathan ya yi magana a shafinsa na Facebook, ya ke cewa shi ya yafe wa Honarabul Aminu Shehu Shagari kamar yadda ya bukata.

“Aminu Shehu Shagari, nagode da hakurin da ka bada. Sai dai ban taba dauka ka yi mani laifi ba.”

Tsohon shugaban kasar ya rubuta: “Abin da na yi cikakken imani da shi, shi ne cewa Ubangiji ya yi amfani da ni ne wajen zartar da kaddararsa.”

KU KARANTA: Manyan Arewa su na shirin babbako da takarar Jonathan a 2023

“Don haka ba ni da makiyan da zan yi fada da su, domin na tabbatar mutane za su iya mani abin da Ubangiji ya ba su dama ne kurum.” Inji Jonathan.

“Ina kiranka da ka cigaba da riko da halin saukin-kai irin na mahaifinka, Marigayi Shehu Shagari, ‘Dan Najeriyan da bai nuna banbamcin kabila.”

Aminu Shehu Shagari wanda ya rike kujerar majalisar wakilai har sau uku, ya goyi bayan ‘dan takarar APC, Muhammadu Buhari a zaben 2015.

‘Dan siyasar ya zabi ya mara wa Muhammadu Buhari baya duk da cewa shi ne ya kifar da mahaifinsa, Shehu Shagari daga kan mulki a 1983.

KU KARANTA: Buhari da Jonathan sun shiga bayan labule a Aso Villa

Ba ni da makiyan fada – Shugaba Goodluck Jonathan ya fadawa Aminu Shagari
Aminu Shagari ya zargi Buhari da yi wa Shagari da Jonathan sharri Hoto: Business Day
Asali: UGC

A karshen jawabinsa, Jonathan ya rubuta: “Allah ya yi maka albarka.” GEJ

Shagari ya ce ya taimaka wajen barka PDP da karya Jonathan a zaben 2015, daga baya ya ce ya gano abin da su ke tunani da gwamnatinsa ba haka ba ne.

Makonni biyu da su ka wuce ne ku ka ji Dr. Goodluck Jonathan, Namadi Sambo da wasu manyan 'yan Najeriya sun ziyarci fadar marigayi Sarkin Zazzau.

Tsohon shugaban kasar ya zo Zariya ne musamman domin yi wa jama'a ta'aziyya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel