Sauran Ma’aikatan Jami’a sun shiga yajin-aiki a kan tsarin IPPIS da kin biyan alawus

Sauran Ma’aikatan Jami’a sun shiga yajin-aiki a kan tsarin IPPIS da kin biyan alawus

- NASU da SSANU sun yi kira ga mutanensu su fara wani yajin aiki a makon nan

- Hakan na zuwa ne a lokacin da gwamnati ta ke kiran a bude duka makarantu

- Ma’aikatan Jami’an su na kuka da IPPIS, sun kuma ce an hana su wasu alawus

Kungiyar NASU ta ma’aikatan jami’an da ba su koyarwa a aji, sun bukaci ‘ya ‘yansu su tafi yajin-aiki da nufin jan-kunnen gwamnatin tarayya.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa NASU ta ce mutanenta su dauke kafa daga zuwa ofis har na tsawon mako biyu daga ranar Litinin.

NASU ta fara wannan yajin-aiki ne a ranar 5 ga watan Oktoba, 2020, bisa zargin matsalolin da ake fuskanta daga manhajar biyan albashi na IPPIS.

KU KARANTA: Buhari ya yi na'am da daukar masu NCE a aikin Gwamnati

Wannan kungiya ta koka da cewa an ki biyan ma’aikatan jami’a bashin kudin da su ke bi daga karin albashin da aka yi a farkon shekarar nan.

Bugu da kari, NASU ta ce akwai wasu alawus da hakkokinta da gwamnati ta ki cika mata.

Kungiyar NASU wanda da farko ta goyi bayan shirin IPPIS, ta kuma ki zuwa yajin aiki, ta bi sahun takwararta ASUU wanda ta dade ta na yajin-aiki.

Jaridar ta ce NASU ta na zargin akwai rashin gaskiya wajen yadda ake gudanar da sha’anin jami’o’in gwamnatin tarayya da ke fadin Najeriya.

Sauran Ma’aikatan Jami’a sun shiga yajin-aiki a kan tsarin IPPIS da kin biyan alawus
Makarantar Jami'a a Najeriya Hoto: Business Day
Asali: UGC

KU KARANTA: Buhari ya kara albashin malaman makaranta a Najeriya

Shugaban kungiyar SSANU na kasa, Kwamred Samson Ugwoke, shi ma ya fitar da jawabi, ya ce ana cin zarafin sauran manyan ma’aikatan jami’a.

Samson Ugwoke ya na zargin malaman jami’a da yi masu ba-ba-ke-re a wajen aiki, abin da SSANU ta ce ya sabawa dokar da ta kafa jami’o’i.

Ba da dadewa ba ku ka ji cewa Gwamnatin tarayya ta bada umurnin bude dukkan wasu makarantu a Najeriya bayan lafawar annobar COVID-19.

Ministan ilmi ya ba duk wasu makarantu masu zaman kansu damar komawa bakin aiki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng