Babbar magana: Sule Lamido ya caccaki Osinbajo, Zulum da sauransu kan hasashen ɓallewar Nigeria

Babbar magana: Sule Lamido ya caccaki Osinbajo, Zulum da sauransu kan hasashen ɓallewar Nigeria

- Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Lamido, ya caccaki wasu shugabannin Najeriya da ke hasashen ballewar kasar

- Mataimakin shugaban kasa Osinbajo da Gwamnan jihar Borno, Zulum na daga cikin shugabannin da tsohon gwamnan ya caccaka

- Sai dai, Osinbajo wanda ya yi magana ta hannun SSG, Boss Mustapha, ya ce an yi wa furucinsa kan ballewar Najeriya bahagon fahimta

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya caccaki mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo kan zargin yin magana game da ballewa da rabuwar Najeriya.

Jaridar ThisDay ta ruwaito cewa Lamido ya kuma caccaki Babagana Zulum, da dattawan kasar, Cif Edwin Clark, Cif Ayo Adebanjo, Janar Theophilus Danjuma da sauran mutanen da suka yi sharhi makamancin wannan kan ballewar Najeriya.

Legit.ng ta tattaro cewa Lamido ya bayyana hakan ne a cikin sakonsa na bikin cikar Najeriya shekaru 60 da samun yancin kai.

Tsohon gwamnan ya yi zantuka masu taba zuciya kan hadin kan Najeriya, cewa kada kasar ta kuskura ta balle duk da banbancin ra’ayi.

KU KARANTA KUMA: Da ɗuminsa: Rundunar soji ta kakkaɓe ƴan bindiga a hanyar Abuja-Kaduna, ta ƙwato makamai

Babbar magana: Sule Lamido ya caccaki Osinbajo, Zulum da sauransu kan hasashen ɓallewar Nigeria
Babbar magana: Sule Lamido ya caccaki Osinbajo, Zulum da sauransu kan hasashen ɓallewar Nigeria Hoto: @Sule_lamido
Asali: Twitter

Ya ce ya zama dole shugabannin Najeriya su san cewa Najeriya ta yi masu rana tsawon shekaru masu yawa.

Sannan ya ce hakkinsu ne su saka wa kasar ta hanyar tabbatar da ganin cewa yan baya masu tasowa ma sun cimma mafarkinsu a karkashin kasa daya.

Rahotannin baya sun nuna cewa Osinbajo ya koka cewa akwai baraka a harkar shugabancin Najeriya da ka iya kawo ballewar kasar har sai an dauki matakin gaggawa.

Osinbajo wanda ya samu wakilcin Boss Mustapha, babbar sakataren tarayya, ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 27 ga watan Satumba a Abuja.

Sai dai, Mustapha ya ce an yi wa furucin nasa a madadin Osinbajo mummunan fahimta.

Mustapha ya ce mataimakin shugaban kasar na ci gaba da jajircewa don ganin Najeriya daya.

KU KARANTA KUMA: Sabbin zafafan hotunan Nafisa Abdullahi kusa da dankareriyar motarta

Har ila yau ya bayyana cewa yana godiya ga kokarin shugaban kasa Muhammadu Buhari a wajen karfafa hadin kan kasar.

A wani labarin, gwamnatin tarayya tayi ala-wadai akan 'yan Najeriyan dake cewa Najeriya na gab da tarwatsewa.

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ya fadi hakan a wata takarda ta ranar Lahadi, 14 ga watan Oktoba wanda yake cewa rashin kishin kasa ne furta hakan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng