Hotunan mutum 11 da Matawalle ya ceto daga hannun 'yan bindiga

Hotunan mutum 11 da Matawalle ya ceto daga hannun 'yan bindiga

- Gwamna Bello Matawalle na Zamfara ya taya mutum 11 da aka ceto daga hannun 'yan bindiga murna

- Ya karbesu hannu bibbiyu a gidan gwamnatin jihar bayan karbosu da aka yi daga hannun 'yan bindigan

- Gwamnan ya sha alwashin cewa ba zai taba sassautawa ba har sai ya ga karshen rashin tsaro a fadin jihar

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya taya mutum 11 murnar karbosu da aka yi daga hannun 'yan bindiga a jihar ba tare da biyan kudin fansa ba.

Wadanda aka ceto din sun hada da maza takwas da mata uku 'yan asalin jihohin Bauchi, Neja, Sokoto da Zamfara.

Hounan mutum 11 da Matawalle ya ceto daga hannun 'yan bindiga
Hounan mutum 11 da Matawalle ya ceto daga hannun 'yan bindiga. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

Matawalle, wanda ya karbesu a gidan gwamnatin jihar a ranar Asabar, 3 ga watan Oktoba, ya tabbatar da cewa mulkinsa ba zai sassauta ba har sai ya tabbatar da wanzuwar tsaro a jihar.

Ya bada umarnin mika dukkan wadanda aka ceto zuwa asibiti domin a duba lafiyarsu kafin su sadu da danginsu.

Hounan mutum 11 da Matawalle ya ceto daga hannun 'yan bindiga
Hounan mutum 11 da Matawalle ya ceto daga hannun 'yan bindiga. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

Hounan mutum 11 da Matawalle ya ceto daga hannun 'yan bindiga
Hounan mutum 11 da Matawalle ya ceto daga hannun 'yan bindiga. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

Hounan mutum 11 da Matawalle ya ceto daga hannun 'yan bindiga
Hounan mutum 11 da Matawalle ya ceto daga hannun 'yan bindiga. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

Hounan mutum 11 da Matawalle ya ceto daga hannun 'yan bindiga
Hounan mutum 11 da Matawalle ya ceto daga hannun 'yan bindiga. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

Hounan mutum 11 da Matawalle ya ceto daga hannun 'yan bindiga
Hounan mutum 11 da Matawalle ya ceto daga hannun 'yan bindiga. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

Hounan mutum 11 da Matawalle ya ceto daga hannun 'yan bindiga
Hounan mutum 11 da Matawalle ya ceto daga hannun 'yan bindiga. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

A wani labari na daban, wata matar aure mai suna Hauwa da ke zama a kwatas ta Diso da ke karamar hukumar Gwale ta jihar Kano ana zarginta da yi wa 'ya'yanta biyu yankan rago.

Hakan ta faru bayan rikicin da ya auku tsakaninta da mijinta mai suna Ibrahim Haruna Aminu wanda bai dade da yin sabuwar amarya ba.

Jaridar Solacebase ta wallafa cewa, yaran da mahaifiyarsu ta yi wa yankan ragon su ne Yusuf Ibrahim mai shekaru 5 da kanwarsa Zahra'u mai shekaru uku.

Wani kawun yaran, Sadiq Haruna Aminu, ya ce Hauwau wacce matar dan uwansa ce kuma mahaifiyar yaran, tana rayuwa cike da hassada da kishi tun bayan da dan uwansa ya auro wata matar, lamarin da yasa ta kashe 'ya'yanta biyu a ranar Asabar.

"Hauwa ta sossoka wa 'ya'yanta wuka wanda hakan ya kawo ajalinsu," Sadiq Aminu yace.

Dagacin Diso, Malam Ahmad Bello, ya nuna razanarsa da aukuwar lamarin ga manema labarai a jihar Kano a ranar Asabar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel