Ondo 2020: Dan Allah ka taka wa Akeredolu birki, PDP ta shawarci Buhari

Ondo 2020: Dan Allah ka taka wa Akeredolu birki, PDP ta shawarci Buhari

- Jam’iyyar PDP ta yi korafi a kan hauhawan rikicin da ake samu a Ondo gabannin zaben gwamna

- Babbar jam’ iyyar adawar ta yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada ya zama dan abi yarima a sha kidan APC da Gwamna Rotimi Akeredolu

- Har ila yau, PDP ta yi ikirarin cewa dan takararta, Jegede Eyitayo, na samun cikakken goyon bayan mutanen Ondo

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi martani a kan yawan rikici da ake ta samu yayinda ake shirye-shiryen zaben gwamnan Ondo.

Babbar jam’iyyar adawar ta yi ikirarin cewa jam’ iyyar All Progressives Congress (APC) na aiki tare da Gwamna Rotimi Akeredolu domin razana dan takararta, Jegede Eyitayo da mutanen jihar.

A shafinta na Twitter, PDP ta shawarci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya daidaita gwamnan na Ondo sannan ya yi amfani da irin dabarun da ya yi amfani da su a Edo don tabbatar da zaben lumana a Ondo.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kama matar da ake zargi da yanka yaranta a Kano

Ondo 2020: Dan Allah ka taka wa Akeredolu birki, PDP ta shawarci Buhari
Ondo 2020: Dan Allah ka taka wa Akeredolu birki, PDP ta shawarci Buhari Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

PDP ta yi kira ga Shugaban kasa da kada ya kula da matsin lambar da yake fuskanta daga Gwamna Akeredolu da APC don shiga lamarin zaben.

Ta ce:

“Don haka kamfen dinmu, na kira ga Shugaban kasa @MBuhari da kada ya ba da kai bori ya hau a kan matsayin lamba da yake samu daga gwamna da ya gaza @RotimiAkeredoluand da @OfficialAPCNg na janye hukucinsa na kin sanya baki a zaben, kamar yadda aka yi a zaben Edo na ranar 19 ga watan Satumba.”

KU KARANTA KUMA: Yadda aka halaka wani matashi kan budurwa a Kano

Ta ci gaba:

“Gwamna @RotimiAkeredolu ya yi wasti da damar da aka basa don haka kada ya ga laifin kowa illa kansa a kan kaye da zai sha a zaben ranar Asabar.

“Da ace Gwamna @RotimiAkeredolu ya yi kokari a shekaru hudu da suka gabata, da yanzu saai dai ya dunga murna kan nasarorinsa maimakon yin barazana ga mutanensa, yana gudu daga nan zuwa chan don yin makudin zabe da kokarin sako fadar Shugaban kasa a ciki.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel