Zaben shugaban ƙasa 2023: Magoya bayan Buhari na son Jonathan ya dawo mulki

Zaben shugaban ƙasa 2023: Magoya bayan Buhari na son Jonathan ya dawo mulki

- Zuwa yanzu dai saura shekaru uku kafin zaben shugaban kasa na 2023 amma tuni batun wanda zai zama shugaban kasa na gaba ya dauki zafi

- Alamu sun nuna wasu magoya bayan Shugaban kasa Buhari na tunanin dawo da tsohon shugaba Goodluck Jonathan

- A bisa rahoton, wadannan masu biyayya na kallon Jonathan a matsayin dan takara da ya cancanci karban mulki daga hannun Buhari idan ya kammala wa’adinsa a 2023

Gabannin zaben shugaban kasa na 2023, an rahoto cewa magoya bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari na duba yiwuwar marawa tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan baya don darewa kujera mafi muhimmanci a kasar.

Jaridar This Day ta ruwaito cewa wannan tunanin shine cewa hakan zai kwantar da hankalin masu matsa lamba don ganin mulki ya koma yankin kudu.

A cewar rahoton, makusantan Buhari na ganin cewa Jonathan ne mutumin da ya fi dacewa da wannan matsayin idan har za a mika shugabancin kasar ga yankin kudu.

KU KARANTA KUMA: Bar murna karenka ya kama kura: Ƙusan APC ya ƙalubalanci nasarar Obaseki

Zaben shugaban ƙasa 2023: Magoya bayan Buhari na son Jonathan ya dawo mulki
Zaben shugaban ƙasa 2023: Magoya bayan Buhari na son Jonathan ya dawo mulki Hoto: @pmnewsnigeria
Asali: Twitter

Wata babbar majiya a sansanin Buhari wacce bata so a bayyana sunanta, ta ce:

“Ya mika mulki cikin lumana sannan bai kullaci kowa da mugun nufi ba saboda haka ba zai zama barazana ga ra’ayin arewa ba.”

Wani dalili da yasa wadannan masu biyayya ga Buhari ke duba yiwuwar marawa shugabancin Jonathan baya a 2023 shine cewa zai yi mulki ne na zango daya.

Wato shekaru hudu kawai, wanda hakan ke nufin mulki zai dawo arewa cikin dan kankanin lokaci.

A cewar masu wannan tunani, idan har wani dan kudu ya yi nasara, yana iya shafe shekaru takwas a kan mulki kafin ya dawo ga arewa.

This Day ta zanta da wasu majiyoyi wadanda ke ganin cewa ba aibu bane don tsohon shugaban kasar ya gaji Buhari.

Wata majiya ta sake tabbatar da ci gaban cewa suna duba yiwuwar dawo da Jonathan wanda ba zai kawo kowani matsala ba.

KU KARANTA KUMA: Daga ƙarshe: Ambasada Wali ya amince ayi sulhu tsakaninsa da Kwankwaso

A cewar wadannan majiyoyi, tsawon shekaru da suka gabata, Buhari da magoya bayansa na kallon tsohon shugaban kasar a matsayin amintacce wanda za a iya dogaro da shi.

Sun bayyana cewa Jonathan ne kadai tsohon Shugaban kasa da ya kasance tare da Buhari a lokacin bikin cika shekaru 60 da samun yancin kai a Eagle Square, Abuja.

A wani labarin, tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ya ce rashin tunani ne zai sa ace shugabanin mulkin soja ne sanadin matsalolin da ke adabar Najeriya.

Tsohon shugaban sojan, mai shekaru 79 ya bayyana hakan ne a cikin sabuwar hirar da ya yi da Channels TV.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel