Kano: Uwa ta yi wa 'ya'yanta yankan rago saboda kishiya

Kano: Uwa ta yi wa 'ya'yanta yankan rago saboda kishiya

- Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kisan kan da wata matar aure ta yi a jihar

- Mahaifiyar 'ya'ya biyu mai suna Hauwa a jihar Kano ta yi wa 'ya'yanta yankan rago da safiyar Asabar

- An gano cewa, hakan ta faru ne sakamakon tsananin kishi da take a kan mijinta ya kara aure

Wata matar aure mai suna Hauwa da ke zama a kwatas ta Diso da ke karamar hukumar Gwale ta jihar Kano ana zarginta da yi wa 'ya'yanta biyu yankan rago.

Hakan ta faru bayan rikicin da ya auku tsakaninta da mijinta mai suna Ibrahim Haruna Aminu wanda bai dade da yin sabuwar amarya ba.

Jaridar Solacebase ta wallafa cewa, yaran da mahaifiyarsu ta yi wa yankan ragon su ne Yusuf Ibrahim mai shekaru 5 da kanwarsa Zahra'u mai shekaru uku.

Wani kawun yaran, Sadiq Haruna Aminu, ya ce Hauwau wacce matar dan uwansa ce kuma mahaifiyar yaran, tana rayuwa cike da hassada da kishi tun bayan da dan uwansa ya auro wata matar, lamarin da yasa ta kashe 'ya'yanta biyu a ranar Asabar.

"Hauwa ta sossoka wa 'ya'yanta wuka wanda hakan ya kawo ajalinsu," Sadiq Aminu yace.

Dagacin Diso, Malam Ahmad Bello, ya nuna razanarsa da aukuwar lamarin ga manema labarai a jihar Kano a ranar Asabar.

Ya ce hakan ta faru ne bayan mahaifin yaran baya nan ya tafi gidan amaryarsa a safiyar Asabar.

Bello ya kushe wannan lamarin, inda yace a maimakon ta kai lamarin kotu, sai ta yanke hukuncin kashe 'ya'yanta da kanta.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna yace rundunar 'yan sandan ta fara bincike.

Amma kuma an tabbatar da cewa, har yanzu ba a ga mahaifiyar ba domin ta tsere.

KU KARANTA: Fyade: Kotu ta kori soja daga aiki, ta yanke masa hukuncin shekaru 5 a gidan yari

Kano: Uwa ta yi wa 'ya'yanta yankan rago saboda kishiya
Kano: Uwa ta yi wa 'ya'yanta yankan rago saboda kishiya. Hoto daga @Solacebase
Asali: Twitter

KU KARANTA: Buhari ya tabbatar da tabarbarewar tattalin arziki da tsaro a Najeriya

A wani labari na daban, wani dan damfarar yanar gizo dake Warri, jihar Delta yace yana amfani da asusun bankunan mutanen kirki wurin adana kudaden damfarar da yayi saboda tsoron hukuma.

John ya ce idan yana jiran wani kudi mai yawa, wanda zai janyo zargin hukuma, yana neman Fastoci su ara mishi asusun bankunan su ya ajiye.

Dan damfarar ya ce, sanin cewa kudade masu kauri suna shiga asusun bankunan Fastoci, ya tabbatar ba za'a zarge su ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel