Buhari: ‘Yan siyasa masu a mutu-ko-ayi-rai ne sanadiyyar tabarbarewar zabe

Buhari: ‘Yan siyasa masu a mutu-ko-ayi-rai ne sanadiyyar tabarbarewar zabe

- Shugaban Najeriya ya yi kuka da barnar da jarababbun ‘Yan siyasa su ke yi

- Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta na kokarin gyara sha’anin zabe

- Shugaban kasar ya ce sakamakon zaben Edo ya nuna cewa da gaske ya ke yi

A ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoba, 2020, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi magane game da harkar magudin zabe a Najeriya.

Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ‘yan siyasa masu matsananciyar buri ne sanadiyyar yin zabe na gaskiya, mai inganci a kasar nan.

Sai dai duk da matsalar da ake samu daga wadannan ‘yan siyasa, shugaban ya ce ya ci aniyar ganin ana gudanar da zabe nagari a mulkinsa.

KU KARANTA: Abin da Jama’a su ke fada game da jawabin Shugaban kasa Buhari

Mai girma Muhammadu Buhari ya yi duk wannan bayani ne a jawabin da ya yi na bikin cika shekaru 60 da samun ‘yancin kan Najeriya.

Buhari ya ce shi mutum ne wanda ya yarda da ingantaccen zabe, har kuma ya ke cewa ya nuna hakan a gwamnatinsa mai-ci tun Mayun 2015.

Ya ke cewa sakamakon zaben kwanan nan na Edo zai karawa ‘yan Najeriya karfin gwiwar gwamnatinsa na ganin kuri’un talaka sun yi tasiri.

“Matsalar sha’anin zabenmu ta na daga mutane ne masu jarabar son mulki, wanda hakan ke jawo jarabar burin samun kujerar gwamnati.” Inji Buhari.

Buhari: ‘Yan siyasa masu a mutu-ko-ayi-rai ne sanadiyyar tabarbarewar zabe
Buhari ya na jawabi Hoto: Channels
Source: UGC

KU KARANTA: ASUU ta ce an yi watanni 7 da hana Malaman Jami’a albashi

“Damukaradiyya a fadin Duniya da yadda na ke kokarin yi a Najeriya, ya na ba mutane karfi.”

Shugaba Buhari ya ce amma idan har wasu sun saida karfinsu, su shirya rasa damarsu, ya kuma ce a shirye ya ke, ya gyara harkar zaben kasar.

Yanzu nan kuma mu ka ji cewa kotu ta rushe hukuncin soke nasarar PDP da Gwamna Douye Diri a Bayelsa, ta yi fatali da karar da jam’iyyar ANDP ta shigar.

Alkalai sun birkitawa jam’iyyar hamayyar lissafi a siyasar Bayelsa da wannan hukunci da aka yi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel