Hukumar PSC kadai ke da ikon daukar ‘Yan Sanda aiki, Kotu ta fadawa IGP

Hukumar PSC kadai ke da ikon daukar ‘Yan Sanda aiki, Kotu ta fadawa IGP

- Kotun daukaka kara ta raba tsohuwar gardamar IGP da Hukumar PSC

- Alkalan babban kotun sun ba PSC gaskiya a kan IGP wajen daukar aiki

- Kotu ta ce Sufetan ‘Yan Sanda bai da ta cewa a harkar daukar dakaru

Kotun daukaka kara ta rusa daukar aikin kuratan ‘yan sanda 10, 000 da sufetan ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya yi a shekarar 2019.

A wani hukunci da wannan kotun daukaka kara mai zama a garin Abuja ta yi, ta ce IGP Mohammed Adamu bai da ikon da zai dauki aiki a doka.

Alkalai uku ne su ka saurari wannan shari’a a karkashin jagorancin Olabisi Ige a ranar Laraba.

KU KARANTA: Shugaban kasa ya turo suna, Wasu ‘Yan Majalisar Dattawa sun ki yin na’am da shi

Jaridar The Cable ta ce Alkalan sun zartar da hukunci cewa daukar sababbin ma’aikatan ‘yan sanda, aikin hukumar jami’an tsaron na PSC ne kawai.

Kafin yanzu kotu ta yanke hukunci a watan Disamban shekarar bara cewa Sufeta Janar na ‘yan sandan kasa ne ya ke da hurumin daukar ‘yan sanda aiki.

Da wannan hukunci, Alkalan kotun daukaka karar, sun yi fatali da shari’ar da babban kotun tarayyar ta yi, inda aka ba IGP Mohammed Adamu gaskiya.

A kara mai lamba ta FHC/ABJ/CS/1124/2019, hukumar PSC ta roki kotu ta tabbatar da cewa IGP bai da ikon daukar aiki ko korar jami’an ‘yan sanda a doka.

KU KARANTA: An yankewa wani daurin shekaru 125 a kan kwangilar karyar shigo da shinkafa

Hukumar PSC kadai ke da ikon daukar ‘Yan Sanda aiki, Kotu ta fadawa IGP
IGP Hoto: P/Times
Source: UGC

A yanzu kotun daukaka kara ta ce an yi kuskure a wancan shari’a, kuma ta ce dokar ‘yan sanda 10, 000 aiki da Sufeta Janar na kasa ya yi, ya ci karo da doka.

Daga yanzu kotu ta rusa daukar aikin wadannan kananan jami’an ‘yan sanda 10, 000 da aka yi a bara.

A wancan lokaci, Alkali Inyang Ekwo na babban kotun tarayya na Abuja, ya yi watsi da wannan bukata a 2019, ya ki rusa daukar aikin da IGP ya fara.

Mai shari’a Inyang Ekwo ya ce sashe na 71 na dokokin ‘yan sanda na 1968 ya daura nauyin daukar aiki ne a karkashin ofishin IGP ba hukumar PSC ta kasa ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel