Rashin nada sabon Sarki ya jefa Zariya cikin dar-dar da tashin hankali

Rashin nada sabon Sarki ya jefa Zariya cikin dar-dar da tashin hankali

- An shafe kwanaki fiye da 10 ba a nada wani sabon Sarki a Zazzau ba

- Gwamnati ta rusa zaben da masu zaben Sarki su ka yi na makon jiya

- Wannan shiru ya jefa al’umma cikin dar-dar da yada jita-jita a Zariya

Jaridar Premium Times ta bayyana cewa an shiga cikin dar-dar da wani hali na dabam yayin da mutanen Zariya da kewaye su ke jiran a nada sabon Sarki.

Hakan na zuwwa ne bayan rasuwar Mai girma Shehu Idris wanda ya rasu a ranar 20 ga watan Satumba, bayan ya shafe shekaru 45 ya na mulkin Zazzau.

Bayan kusan mako guda da rasuwar Shehu Idris, iyalansa sun bar gidan sarauta. Legit.ng ta samu labari iyalin marigayin sun koma wani gidansa a cikin gari.

Wata majiya ta ce Idris ya bar ‘ya ‘ya 32, jikoki 168, da tattaba-kunne 36 a lokacin rasuwarsa.

KU KARANTA: Abin da ya jawo jinkiri wajen nada sabon Sarki a Zazzau - Masana

Da aka yi zabe Bashir Aminu ne ya zo na farko, sai Munir Ja’afaru a bayansa, Turakin Zazzau ya zo na uku ne, yayin da aka yi waje da; Magajin Garin Zazzau.

Daga baya gwamnatin Kaduna ta rushe wannan zabe da aka yi, bisa zargin hana wasu ‘yan takara shiga zaben, ta kuma ce an fara sabon shirin nadin sabon Sarki.

Wannan zama shiru ba tare da Sarki ba, ya jawo rade-radi iri-iri a yankin Zariya da kewaye.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa tun a safiyar ranar Lahadi, jama’a su ka yi ta yada jita-jitar an zabi Yariman Zazzau, Munir Ja’afaru a matsayin Magajin Shehu Idris.

A lokacin an baza jami’an tsaro a gidan Yariman, zuwa yanzu da-dama ba su nan. Rahotanni sun tabbatar da Jafaru ya yi tafiya a makon nan zuwa garin Kaduna.

Rashin nada sabon Sarki ya jefa Zariya cikin jita-jita, dar-dar da tashin hankali
Tsohon Sarki Shehu Idris Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Ahmad Gumi ya fadi hanyar zaben shugaba a musulunci

A gefe guda kuma masoyan Magajin Garin Zazzau su na ta wallafa hotunansa, su na yi masa addu’ar Allah ya ida nufi, har wasu na cewa lokaci kawai ake jira.

Mun samu labarin cewa wani daga cikin ‘yan takarar ya na ganin cewa gwamnatin jihar Kaduna ta na bakin kokarinta ne na ganin ta hana shi darewa gadon mulki.

Rahotanni sun ce akwai wanda ya ke shirin shiga kotu da gwamnati idan aka hana shi kujerar.

Idan za ku tuna manyan masu neman sarautar a yanzu su ne: Iyan Zazzau, Bashir Aminu; Magajin Garin Zazzau, Ahmed Bamalli; Yeriman Zazzau, Munir Ja’afaru.

Haka zalika babban ‘dan marigayin, Turakin Zazzau, Aminu Idris ya na cikin masu harin gadon.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel