Sanwo-Olu: Mu na tunanin gina gadar da za ta hada Legas da kuma Jihar Ondo

Sanwo-Olu: Mu na tunanin gina gadar da za ta hada Legas da kuma Jihar Ondo

- Babajide Sanwo-Olu ya ce su na shirin kusanto da Ondo zuwa Jihar Legas

- Gwamnan ya ce za su gina gada ta yankin ruwa da za ta rage tafiya a yankin

- Amma Sanwo-Olu bai bayyana yadda za a tsara wannan gagarumin aiki ba

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana shirinsa na ganin an samu doguwar gadar da za ta hada jiharsa da makwabciyarsa Ondo.

Mai girma Babajide Sanwo-Olu ya bayyana cewa gwamnatin APC ta na tunanin hada Legas da Ondo ta ruwa domin rage cinkoso a kan tituna.

Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 28 ga watan Satumba, lokacin da APC ta shiga garin Okitipupa domin yakin neman zabe a Ondo.

KU KARANTA: ‘Dan takarar APC ta fallasa yadda PDP ta lashe zaben Edo da kashe-kashe

Babajide Sanwo-Olu shi ne aka zaba a matsayin sarkin yakin jam’iyyar APC a zaben Jihar Ondo.

“Gwamnatin APC ta na tunanin kirkiro gadar da za a gina da za ta hada jihohin Legas da Ondo ta yankin IIaje.” Inji Mista Babajide Sanwo-Olu.

Gwamnan na Legas ya bayyana cewa idan aka yi nasarar yin wannan gada, lokacin da jama’a su ke batawa a hanyar Legas zuwa Ondo za ta ragu.

Ya ce: “Idan an yi hakan, zai sa matafiya su rika cin mintuna 30 ko makamancin haka su isa Legas.”

KU KARANTA: Wasu Yarbawa sun yi watsi da Tinubu, za su yi Ibo a 2023

Sanwo-Olu: Mu na tunanin gina gadar da za ta hada Legas da kuma Jihar Ondo
Babajide Sanwo-Olu da Babajide Sanwo-Olu Hoto: Pulse
Asali: UGC

Jihohin su na makwabtaka da juna a kudu maso yammacin Najeriya. Matafiya su kan ci sa’a biyar a kan titin Legas zuwa Ondo mai kilomita 250.

A kokarin jawo hankalin jama’a su zabi jam’iyyar APC a zaben gwamnan Ondo, Sanwo-Olu ya ce Rotimi Akeredolu ba zai ci amanar jama’a ba.

Mai girma gwamnan ya tabbatarwa mutanen karamar hukumar Okitipupa cewa Akeredolu da Lucky Aiyedatiwa za su cika alkawarin da su ka yi.

Kwanaki kun ji an yi ta rade-radin baraka a jam’iyyar APC a yankin kudu maso yamma inda Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ke da karfi sosai.

Daga baya Bola Ahmed Tinubu ya fito ya yi watsi da rahotannin rigima da Rauf Aregbesola.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng