Gwamna Okowa ya yabi Shugaban kasa a kan aikin dogon Warri zuwa Itakpe

Gwamna Okowa ya yabi Shugaban kasa a kan aikin dogon Warri zuwa Itakpe

- Gwamna Ifeanyi Okowa ya yabawa irin salon mulkin Shugaba Muhammadu Buhari

- Okowa ya gode da gwamnatin APC ta yi wa Delta titin dogon Itakpe-Ajaokuta-Warri

- Gwamnan ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta samar da isasshen tsaro a jirgin kasan

A ranar Talata, 29 ga watan Satumba, gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Buhari na rashin nuna banbamci.

Sanata Ifeanyi Okowa ya ji dadin yadda gwamnatin Muhammadu Buhari ta kammala aikin jirgin kasan Itakpe-Ajaokuta-Warri mai tsawon kilomita 326.

Gwamnan ya yi wannan jinjina ne a lokacin da aka kaddamar da aikin dogon Itakpe zuwa Warri, wanda gwamnati ta sa wa sunan Dr. Goodluck Jonathan.

KU KARANTA: Buhari ya kaddamar da jirgin kasan Warri-Itakpe daga Abuja

Shugaban kasa ya kaddamar da wannan aiki ne jiya a garin Owa-Oyibu da ke garin Ika, jihar Delta.

Ifeanyi Okowa ya mika godiyarsa ga gwamnatin Buhari a madadin mutanen Jihar Delta musamman mazauna yankin karamar Ika ta Arewa a jiya.

Ga abin da ya ke cewa:

“Mutanen Delta su na farin ciki zuwan wannan rana, Jama’an Ika su na murna da karrama tsohon shugaban kasa da aka yi, na sa wa dogon Owa-Oyibu sunansa.”

KU KARANTA: Hukumar NERC ta umarci DISCOs su janye karin kudin wuta

Gwamna Okowa ya yabi Shugaban kasa a kan aikin dogon Warri zuwa Itakpe
Gwamna Okowa da Ministan sufuri Hoto: Twitter/IAOkowa
Asali: Twitter

“Mu na murna a matsayinmu na mutanen nan saboda jirgin kasan zai yi sanadiyyar bunkasa kasuwanci, ya kuma zama sauki ga masu karamin karfi.” Inji Okowa.

Gwamnan ya kuma yi magana game da sha’anin tsaro, “Ya na da muhimmanci gwamnatin tarayya da hadin-kan jihohin, sun samar da tsaro a tsakanin dogon.”

A baya gwamnatin tarayya ta yi alkawari za ta gama aikin dogon jirgin kasan kafin 2019. An shafe shekaru 30 ana jiran a kammala wannan aiki.

Wannan alkawari da ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya yi, bai samu cika ba sai zuwa yanzu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel