Kasafin kudi: ‘Yan Majalisa sun ce za su hukunta Hukumomin da ke saba doka

Kasafin kudi: ‘Yan Majalisa sun ce za su hukunta Hukumomin da ke saba doka

- Majalisar Tarayya ta yi magana a kan MDAs da ke kin yin ayyukan da aka tanada

- Ana warewa wasu Ma’aikatu kudi a kasafin kasa, amma su gagara cika alkawari

- Femi Gbajabiamila ya ce yin hakan babban laifi ne, kuma za a hukunta masu laifin

A ranar 29 ga watan Satumba, 2020, majalisar wakilan tarayya ta yi barazanar hukunta ma’aikatun da su ka gaza yin ayyukan da aka ba su kudinsu.

Majalisar wakilai ta koka game da ma’aikatu da hukumomin da ake warewa kudi a kasafin shekara da sunan za ayi aiki, amma su gaza yin ayyukan.

Wannan gargadi da majalisar wakilan kasar ta yi ya fito ne ta bakin kakakinta, Femi Gbajabiamila.

KU KARANTA: Kasashen da ake samun aikin-yi cikin sauki

Da ya ke jawabi a ranar Talata, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, ya ce kin yin ayyukan da su ke cikin kundin kasafin kudi, cin amanar al’ummar Najeriya ne.

Gbajabiamila ya ke cewa masu yin wannan danyen aiki su na jawo abin da zai sa jama’a su daina yadda da gwamnati, tare da kuma kawo rashin cigaba.

Rt. Hon. Gbajabiamila ya ke jan-kunnen ma’aikatu da su san cewa kundin kasafin kudi ba takarda ba ce kurum, doka ce wanda ake bukatar ‘yan kasa su bi.

A cewar shugaban majalisar, “Batar da kudi a wajen kasafin kasa laifi ne, kamar kuma yadda ya ke laifi a ki yin ayyukan da aka ware masu kudinsu.”

Kasafin kudi: ‘Yan Majalisa sun ce za su hukunta Hukumomin da ke saba doka
Buhari a Majalisa Hoto: Punch
Asali: UGC

KU KARANTA: Za mu rika rabawa Marasa karfi N5, 000 duk wata a Bayelsa – Minista

Haramun ne kashe sisin kobo ba tare da ya bi ta hannun ‘yan majalisa a Najeriya ba. Sannan karbar kudin ayyuka ba tare da an yi ba, ya sabawa dokar kasa.

Shugaban majalisar ya tabbatar da cewa Majalisa za ta yi aiki da bangaren zartarwa wajen kawo tsare-tsare da dabbaka shirin da za a amfana da dukiyar mai.

A baya kun ji cewa sanotoci sun ki amincewa da, Aisha Umar, wanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zaba ta rike shugaban kujerar PENCOM.

Wannan Baiwar Allah da Shugaban kasar ya zaba ta gaza samun karbuwa a Majalisar dattawa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng