Abin takaici ne Bayelsa ta ce a daina biyanmu kudin rijiyoyinmu inji Wike
- Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya yi wa Sanata Douye Diri raddi
- Gwamnan Bayelsa ya na so a daina biyan Ribas kudin rijiyoyin Soku
- Nyesom Wike da kuma Gwamna Douye Diri duk ‘Yan jam’iyyar PDP ne
Jihohin Ribas da Bayelsa sun dawo da gabarsu a kokarin mallakar rijiyoyin man Soku da ke karamar hukumar Akuku-Toru, jihar Ribas.
A watan Disamban shekarar da ta wuce 2019, wani Alkalin babban kotun tarayya ta yanke hukunci cewa rijiyoyin man Soku na jihar Ribas ne.
A dalilin wannan hukunci, kotu ta umarci hukumar RMAFC mai alhakin kason arziki da albashi da ta rika biyan Ribas la’adar rijiyoyin man ta.
Sabon gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri ya soki wannan shari’a, ya kuma daukaka karar zuwa babban kotun daukaka kara na tarayya.
KU KARANTA: Dokar da Buhari ya kawo ta sa Gwamnoni sun maka shi a kotun koli
Gwamnan Ribas, Nyesom Wike ya maidawa takwaran na sa martani, ya nuna cewa bai yarda da ikirarin da gwamnatin Douye Diri ta ke yi ba.
Nyesom Wike ya bayyana haka ne a lokacin da shugaban hukumar RMAFC, Alhaji Mohammed Usman, ya kai masa ziyara a gidan gwamnati.
Wike ya bukaci RMAFC ta cigaba da biyan gwamnatin Jihar Ribas kason da aka samu daga rijiyoyin man Soku, ta yi watsi da Douye Diri.
“Abin takaici ne da gwamnan Bayelsa, ya fada maku cewa ku daina biyanmu kasonmu da aka samu daga rijiyoyin man Soku lokacin da ku ka ziyarcesa.”
KU KARANTA: APC ta soki shari'ar da aka yi a jihar Bayelsa
Ya ce: “Maganar ta na gaban kotun koli lokacin da hukumar raba iyaka ta yarda cewa ta yi kuskure wajen jefa rijiyoyin man Soku a jihar Bayelsa.”
“Don haka aka umarci hukumar ta gyara kuskurenta a bugun da ta yi na 12. Lokacin da su ka gaza gyara kuskuren, dole mu ka kai su kotun tarayya.”
Gwamna Diri ya nemi gwamnati ta daina biyan gwamnatin Ribas wani kudi har sai lokacin da aka karkare shari’a a kotu, abin da Wike bai yi na’am da shi ba.
A baya kun ji cewa masanan Majalisar Dinkin Duniya su na so gwamnatin Najeriya ta saki Matashin nan mai laifin batanci, Yahaya Shariff-Aminu.
Wasu manya a majalisar dinkin Duniyan sun huro wuta a kan fito da Yahaya Shariff-Aminu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng