Zan sauka daga Gwamna idan Amaechi ya nuna aiki ɗaya da yayi wa Rivers - Wike
- Gwamna Nyesom Wike ya yi watsi da sukar da ya sha daga Rotimi Amaechi, ministan sufuri game da shugabanci a jihar Ribas
- Wike ya bukaci Amaechi da ya bayyana gudunmawar da ya ba jihar a matsayinsa na minister
- Gwamnan ya kuma nuna rashin yarda da cewar alkalai da bangaren shari’a sun rasa muryoyinsu a Ribas
Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya bayyana cewa ya shirya sauka daga kujerar shugabanci idan Rotimi Amaechi, ministan sufuri ya ambaci gudunmawarsa ga jihar a matsayinsa na wanda ke rike da mukamin minista.
A cewar jaridar The Cable, Wike ya yi furucin ne a ranar Litinin, 28 ga watan Satumba, a lokacin wata hira a tashar AIT.
KU KARANTA KUMA: 'Yan sintiri ga FG: A shirye muke mu kawar da 'yan ta'adda da 'yan bindiga
Furucin gwamnan ya kasance martani ne ga ikirarin Amaechi na cewa shi (Amaechi) ya kasance daya daga cikin gwamnoni mafi nagarta da jihar ta samu.
An tattaro cewa Amaechi ya yi furucin ne a ranar Lahadi, 27 ga watan Satumba, a wajen taron binne Adolphus Karibi-Whyte, wani tsohon alkalin kotun koli.
Ministan ya yi korafin hauhawan rashin tsaro, rashin kyawun hanyoyi da razana bangaren shari’a a jihar Ribas.
Amma a martaninsa, Wike ya ce shi ya kawo tarin ci gaba a Ribas yayinda yake rike da mukamin karamin ministan ilimi, yayinda Amaechi ba zai iya bugan kirji kan kowani nasara ba.
Wike ya ce:
“Kai minista ne, ka fada ma mutanen Ribas cewa na kawo wannan, ambaci abu daya. Idan ka ambata, zan yi murabus yanzun nan. Ambaci abunda ka kawo wa mutanen Ribas don gamsar da su. Muna da ilimi sosai da ba za ka iya yaudararmu ba.”
KU KARANTA KUMA: Najeriya ta rubuta takarda zuwa ga Xi Jinping domin taya Sinawa murna
Gwamnan ya kuma yi watsi da ikirarin Amaechi na cewa alkalai da bangaren shari’a sun rasa muryoyinsu a jihar, jaridar The Sun ta ruwaito.
Ya yi zargin cewa ministan ya rufe kotun tsawon shekaru biyu a lokacin da yake gwamna.
A wani labari na daban, Ministar bada tallafi da agaji da cigaban al’umma, Hajiya Sadiya Umar-Faruk, ta kaddamar da shirin CCT na gwamnatin tarayya a jihar Bayelsa.
Sadiya Umar-Faruk ta ce gwamnati za ta rika biyan marasa hali N5000 duk wata a Bayelsa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng