Jihohi sun kai karar Gwamnatin Tarayya kan dokar E.O 0010 ta daukar dawainiyar kotu

Jihohi sun kai karar Gwamnatin Tarayya kan dokar E.O 0010 ta daukar dawainiyar kotu

- Gwamnoni sun kai karar gwamnatin tarayya a babban kotun koli na kasa

- Jihohin Najeriya su na kuka da dokar EO 0010 da shugaba Buhari ya kawo

- A cewarsu wannan doka ta ci karo da kundin tsarin mulki da dokar kasa

Jihohin Najeriya 36 sun tafi gaban kotun koli, su na kalubalantar doka mai cikakkiyyar iko ta shugaban kasa, mai lamba ta 00-10.

Gwamnonin za su gwabza da shugaban kasa Muhammadu Buhari a gaban kuliya, game da yadda za a rika tafiyar da harkar kotu a kasar.

Duka gwamnonin jihohin kasar nan 36 sun gabatar da wannan kara a babban kotun kasa na koli ne ta hannun kwamishinonin shari’arsu.

Jihohin su na so a Alkali ya yi fatali da dokar 0010 ta shugaban kasa Buhari da nufin cewa ta ci karo da kundin tsarin mulki da dokar kasa.

KU KARANTA: Buhari ya kai wa ‘Yan Majalisa kudirin PIB, zai kashe NNPC

Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami ne kadai wanda karar ta ambata, domin ya kare gwamnati.

Manyan lauyoyi tara su ka tsayawa gwamnonin jihohin a karkashin jagorancin tsohon shugaban kungiyar NBA, Augustine Alegeh SAN.

Augustine Alegeh SAN da sauran lauyoyi shida a madadin jihohin sun ce gwamnati ta bar su da dawainiyar manyan kotun da ke Najeriya.

Gwamnonin sun koka da yadda aka yi amfani da wannan doka wajen daurawa jihohin alhakin kula da albashi da kudin ayyukan wadannan kotu.

KU KARANTA: Gumi ya ci gyaran Buhari a kan dokar kullen COVID-19

Jihohi sun kai karar Gwamnatin Tarayya kan dokar E.O 0010 ta daukar dawainiyar kotu
Gwamnoni wajen taron NGF Hoto: Pulse
Source: UGC

jaridar Vanguard ta ce kotun da gwamnonin jihohin su ka ce an bar su da nauyinsu sun hada da babban kotun jiha, da kotun daukaka karar shari’a.

Lauyoyin da su ka tsayawa gwamnatin tarayya su na ikirarin dokar da Buhari ya kawo ta sabawa sashe na 6 da na 8 na kudin tsarin mulkin kasa.

A karkashin sassa na 6 da 8 na dokar Najeriya, daukar nauyin wadannan kotu da aka ambata duk sun rataya ne a kan wuyan gwamnatin tarayya.

Masu karar su na so gwamnatin tarayya ta biya su kudin da su ka kashe a kan kotunan tun 2009.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel