Yanzu yanzu: Mayaƙan Boko Haram sun sake kaiwa tawagar Gwamna Zulum hari ranar Lahadi

Yanzu yanzu: Mayaƙan Boko Haram sun sake kaiwa tawagar Gwamna Zulum hari ranar Lahadi

- Mayaƙan Boko Haram sun sake kaiwa tawagar Gwamna Zulum hari a yankin Monguno-Maiduguri

- Sabon harin na zuwa ne a yau Lahadi, 27 ga watan Satumba, sa'o'i 48 bayan wanda suka kai masa a Monguno

- Sai dai ba a rasa rai ko guda ba kamar yadda majiya ta bayyana

Yan ta’addan Boko Haram sun sake kaiwa ayarin motocin gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, wadanda ke a hanyarsu ta dawowa harin bazata a yankin Monguno-Maiduguri.

Sabon harin ya afku ne a yammacin ranar Lahadi, 27 ga watan Satumba, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Harin na zuwa ne sa’o’i 48 bayan yan Boko Haram sun kai wa motocin gwamnan hari a hanyar Kauwa-Baga, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Yanzu yanzu: Mayaƙan Boko Haram sun sake kaiwa tawagar Gwamna Zulum hari ranar Lahadi
Yanzu yanzu: Mayaƙan Boko Haram sun sake kaiwa tawagar Gwamna Zulum hari ranar Lahadi Hoto: @vanguardngrnews
Source: Twitter

Garin Monguno na a kimanin kilomita 80 zuwa Maiduguri.

Har ila yau garin na dauke da dubban yan gudun hijira wadanda mafi akasarinsu sun fito ne daga Marte, Baga, Kukawa, Dikwa da sauran kananan hukumomi da ke kewaye.

KU KARANTA KUMA: Sabon sarkin Zazzau: Na shiga littafi na uku kuma na karshe, inji El-Rufai

Majiyoyi sun bayyan cewa harin ya yi sanadiyar harbin tayar baya na motar bas da ke dauke da yan jaridar da ke tare da gwamnan, amma direban ya yi kokari ya tuka motar da fasasshen taya domin tsira daga lamarin.

Sai dai babu cikakken labarin kan lamarin a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Amma daya daga cikin yan jaridar da abun ya cika da shi, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa motocin ta sake riskar wani hari na Boko Haram kimanin kilomita 50 zuwa Maiduguri.

Sai dai kuma, wayar dan jaridar ta mutu saboda rashin kyan cibiyar sadarwa, amma binike ya nuna cewa babu wanda ya rasa ransa a wannan sabon harin.

KU KARANTA KUMA: Harin zaben 2023: Kwamitin ɗinke ɓarakar PDP ya gana da Babangida a Minna

A baya mun ji cewa, hedkwatar tsaro ta ce mutum 18 yan ta’addan Boko Haram suka kashe a wani harin bazata da suka kai kan ayarin motocin gwamnan jihar Borno a ranar Juma’a.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel