Yan bindiga sun sake kashe wani babban kanal din soji a Katsina

Yan bindiga sun sake kashe wani babban kanal din soji a Katsina

- Rundunar sojin Naeriya ta sake rashi na wani kanal dinta da wasu jami'ai biyu

- Lamarin ya afku ne a wani musayar wuta da aka yi tsakanin sojoji da yan bindiga a kauyen Unguwar Doka da ke karamar hukumar Faskari

- Sojojin ma sun kashe yan bindiga da dama a harin sannan sun samo wasu kayayyaki

Yan bindiga sun kashe wani kanal din rundunar sojin Najeriya, M.Z Manu da wasu sojoji biyu a kauyen Unguwar Doka da ke karkashin karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.

An tattaro cewa yan bindigan, dauke da bindigogin AK-47 sun kai mamaya kauyukan a daren ranar Alhamis sannan suka fara harbi ba kakkautawa.

A cikin haka ne aka kashe babban jami’in sojan da wasu sojoji yan farar hula, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Mukaddashin labarai na ayyukan rundunar tsaro, Birgediya Janar Benard Onyeuko, ya tabbatar da afkuwar lamarin a cikin wata sanarwa ga manema labarai a babban sansanin soji IV Faskari.

Ya ce rundunar Operation Sahel Sanity sun amsa wani kira mai cike da damuwa a ranar 24 ga watan Satumba, cewa yan bindiga sun kai hari kauyen Unguwar Doka sannan aka turasu yankin inda suka kakkabe yan bindigan.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: Sojin Najeriya sun ragargaza 'yan ta'adda a sansaninsu a Borno (Bidiyo)

Yan bindiga sun sake kashe wani babban kanal din soji a Katsina
Yan bindiga sun sake kashe wani babban kanal din soji a Katsina Hoto: People Gazatte
Source: UGC

A yayin arangamar, dakarun soji sun kashe yan bindiga 21 yayinda sauran suka tsere cikin jeji da raunukan harbin bindiga.

Jawabin ya bayyana cewa sojoji sun ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su, ciki harda jariri dan wata takwas wanda ya shafe sama da kwanaki 23 a hannun yan bindigan.

Har ila yau sun kuma samo bindigar AK-47 guda daya da babura uku daga hannun yan ta’addan.

KU KARANTA KUMA: Marigayi Mai Deribe: Hotuna da bidiyon gidan zinarin hamshakin mai kudin arewacin Najeriya

“Sai dai cike da bakin ciki, sakamakon arangamar da aka yi da yan bindigan, an rana babban soja guda da wasu sojoji biyu, sannan wasu soji biyu sun ji rauni kuma a yanzu haka suna samun kulawa a wani cibiyar kiwon lafiya na soji kuma suna samun sauki,” in ji Onyeuko.

“Dakarun sojin marasa tsoro na ci gaba da fatattakar yan bindiga cikin jeji sannan sun mamaye yankunan gabaki daya tare da yin sintiri don hana su katabus,” ya kara da cewa.

A gefe guda, mun ji cewa samamen da dakarun sojin sama na rundunar Operation Lafiya Dole suka aiwatar suke aiwatar ya cigaba da bada sakamako mai kyau.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel