Uzodinma: Ka yi shiru, ba ka nan lokacin da ake gwagarmaya a APC inji Kawu Sumaila

Uzodinma: Ka yi shiru, ba ka nan lokacin da ake gwagarmaya a APC inji Kawu Sumaila

- Kawu Sumaila ya ce ya kamata a ladabtar da duk masu kawowa APC cikas

- Tsohon ‘Dan Majalisar ya soki surutun da Hope Uzodinma ya ke yi a APC

- Sumaila ya ce Gwamnan Imo bai da hurumin da zai yi magana a Jam’iyya

Abdulrahman Kawu Sumaila, tsohon Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya caccaki gwamnan Imo, Hope Uzodinma, kan magana a madadin ‘yan APC.

Hon. Abdulrahman Kawu Sumaila ya bayyana cewa gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma bai cancanta ya bude baki ya yi magana da yawun bakin jam’iyyar APC ba.

Tsohon ‘dan majalisar ya na ganin cewa Sanata Hope Uzodinma bai da ilmin da zai ce wani abu da sunan APC, domin a lokacin da aka kafa wannan jam’iyya ba ya nan.

Bayan rashin sanin gwagwarmayar da aka yi wajen kafa APC, Abdulrahman Kawu Sumaila ya ce mai girma Hope Uzodinma bai yi yawon bin jam’iyya wajen kamfen ba.

KU KARANTA: ‘Dan Majalisar APC ya ce zai sa a ba wani kashi saboda zaginsa a Facebook

Jaridar The Cable ta ce Hon. Kawu Sumaila ya yi kira ga uwar jam’iyya ta duba duk matsalolin cikin gidan da ake fama da su tun 2019, da niyyar kawo karshen rigingimun.

Da ya ke magana da manema labarai a Kano, Kawu Sumaila ya ce Uzodinma bai san lokacin da aka yi ta fadi-tashi domin ganin jam’iyyar APC ta kai ga ci a baya ba.

“Ina ganin lokaci ya yi da APC za ta duba, ta gano wadanda su ka jawowa jam’iyya matsala. Ya kamata su yabawa aya zaki, kuma an fara ne daga 2019 zuwa yanzu.” Inji sa.

Sumaila ya ce “Duk wanda bai gamsu da hukuncin da jam’iyya ta dauka ba, ya kai kara kotu.”

KU KARANTA: Gwamnatin PDP ta na zargin tsohon Gwamnan Zamfara da karkatar da N37bn

Uzodinma: Ka yi shiru, ba ka nan lokacin da ake gwagarmaya a APC inji Hon. Sumaila
Uzodinma da Buhari Hoto: Twitter/@ngrpresident
Source: Facebook

Gogaggen ‘dan siyasar ya kara da cewa: “Babatun da gwamnan Imo, Hope Uzodinma ya ke yi, rashin adalci ne, domin tun farko bai san ta yadda aka kafa jam’iyyar APC ba.”

“Ban taba ganinsa ya na bin Buhari wurin yakin neman zabe ba, don haka bai san mecece APC ba.”

Dazu kun ji cewa tsohon shugaban APC, Adams Oshiomhole ya yi magana game da nasarar da jam'iyyar PDP a Edo, ya ce shan kashin APC bai kai shi kasa a siyasa ba.

A jawabinsa, Sumaila ya ce saura kiris Adams Oshiomhole ya kai jam’iyyar APC makarbata

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel