Sarkin Zazzau ne ya taimaka min sulhunta masu rikici a Plateau - Olusegun Obasanjo

Sarkin Zazzau ne ya taimaka min sulhunta masu rikici a Plateau - Olusegun Obasanjo

- Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce marigayi Sarkin Zazzau, Shehu Idris ya taimakawa gwamnatinsa sosai

- Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya yi wurin addu'ar uku da aka shirya don marigayin a ranar Laraba

- A jawabinsa, Gwamna El-Rufai ya ce gwamnatinsa ta yi babban rashin uban kasa mai bada shawarwari a kan batutuwa da dama

Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana yadda marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ya taimaka masa a lokacin yana shugaban kasa.

Obasanjo: Yadda marigayi sarkin Zazzau ya min wani taimako a lokacin da babu wanda zai iya taimaka min
Olusegun Obasanjo: Hoto daga @Cableng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamnati, 'yan sanda da kungiyar kwadago sun bukaci mutanen Katsina su kare kansu daga 'yan bindiga

Obasanjo ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 23 ga watan Satumba a Zaria, jihar Kaduna yayin addu'ar uku aka shirya don marigayin kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito.

Ya yi bayanin cewa tsohon sarkin ya taimaka masa sosai a lokacin yana shugaban kasar Najeriya.

Tsohon shugaban kasar ya ce:

"Ya taimaka min wurin tafiyar da harkokin kasar nan.

"Na tuna lokacin da rikicin Plateau ta taso. Bani da wanda zai taimaka min wurin yin sulhu a kan rikicin da aka dade ana yi, sai na kira shi.

"Marigayi sarki mutum ne mai son zaman lafiya da sulhunta mutane; mutum ne wanda baya nuna banbancin na addini, kabila ko matsayi na rayuwa."

KU KARANTA: Fitar da bidiyon lalata na budurwa ya saka ango ya fasa aurenta a Sokoto

A jawabinsa, gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya ce gwamnatin jihar ta yi rashin mai bada shawara kuma abin dogaro.

"Gwamnatin jihar Kaduna ta amfana da shawarwari da hikima irin ta sarki saboda ya yi aiki da gwamnoni 20 da suka shude a jihar Kaduna."

A wani labarin daban, Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido-Sanusi, a ranar Talata ya ce 'yan Najeriya suna korafi a kan karij kudin lantarki da aka yi a baya bayan nan ne saboda ba su da tabbacin za su more kudinsu.

Da ya ke jawabi a wurin taron masu saka hannun jari karo na 5 da aka yi a Kaduna, Sanusi ya yi bayanin cewa 'yan Najeriya da dama har da masu treda a shirye suke su biya kudin idan har za a sika samun wutar yadda ya dace domin su inganta sana'ar su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel