Zargin $6m: Felix Okpoh ya kawo kan shi hannun Hukuma inji Jami’in EFCC

Zargin $6m: Felix Okpoh ya kawo kan shi hannun Hukuma inji Jami’in EFCC

- Felix Osilama Okpoh ya mika kan shi gaban hukuma a karshen makon jiya

- Ana zargin wannan Bawan Allah da laifin damfarar Bayin Allah a Amurka

- Matashin da ake nema a Duniya ya ce darajar iyayensa ta sa ya ke son tuba

Wani mutumin Najeriya mai suna Felix Osilama Okpoh, wanda ake nema a kasar Amurka bisa zargin damfara, ya mika kansa da kansa gaban hukuma.

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta ce Mista Felix Osilama Okpoh ya kawo kansa gabanta a makon da ya wuce.

EFCC ta ce Felix Osilama Okpoh ya sallama kansa ne a ranar 18 ga watan Satumba, 2020. Wannan jawabi ya fito ta bakin kakakin hukumar, Wilson Uwujaren.

KU KARANTA: EFCC ta kama dan damfarar da ake nema a kasar waje

Wilson Uwujaren ya shaidawa ‘yan jarida cewa yanzu jami’ai sun fara gudanar da bincike a game da zargin laifuffukan da ke kan wuyan wannan Bawan Allah.

Ana zargin Felix Osilama Okpoh mai shekaru 31 a Duniya da hannu wajen damfarar mutane fiye da 50 a Amurka ta hanyar aika masu sakon bogi a akwatin Email.

Wanda ake zargin ya hada baki da wasu mutane biyar, ya damfari mutanen Amurka kudin da su ka haura Dala miliyan shida, fiye da Naira biliyan biyu kenan.

KU KARANTA: An yi ram da wani gawurtaccen dan damfara a Najeriya

Zargin $6m: Felix Okpoh ya kawo kan shi hannun Hukuma inji Jami’in EFCC
Felix Osilama Okpoh
Source: UGC

Hukumar kasar ta ce mahaifin wannan mutumi, Kanal Garuba Okpoh da kuma mahaifiyarsa, Justina Okpoh ne su ka yi masa rakiya zuwa ofishinsu na Legas.

Mista Okpoh ya bayyanawa jami’an da ke bincikensa cewa ya kawo kanshi ne saboda mutuncin iyayensa da ya ke gani, da kuma son ya gama da Duniya lafiya.

FBI ta na zargin Okpoh da bada lambar asusun daruruwan jama’a ga wasu ‘yan damfara. A sanadiyyar haka aka sulale da kudin jama’a ba tare da an ankara ba.

A watannin baya kun ji yadda Hukumar EFCC ta hada kai da FBI ta Amurka domin a cafke Anthony Osaro wanda ya addabi jama’a da zamba da kuma damfara.

Mista Anthony Osaro ya na da shekaru 22 ne rak da haihuwa, amma ya addabi Bayin Allah.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel