Lekan Ojo ya daurawa Tinubu da Oshiomhole laifin shan kashi a hanun PDP

Lekan Ojo ya daurawa Tinubu da Oshiomhole laifin shan kashi a hanun PDP

- Wani daga cikin manyan APC, ya yi magana game da zaben Gwamnan Jihar Edo

- Jackson Lekan Ojo ya soki rawar da Adams Oshiomhole da Bola Tinubu su ka taka

- ‘Dan siyasar ya ce al’ummar Edo sun ki zaben APC ne saboda tsoma bakin Tinubu

Kusa a jam’iyyar APC, Jackson Lekan Ojo ya tofa albarkacin bakinsa a game da yadda sakamakon zaben gwamnan jihar Edo da aka yi ya kasance.

Mista Jackson Lekan Ojo ya zargi manyan jagororin APC na kasa, Adams Oshiomhole da kuma Bola Tinubu da jawowa jam’iyyar APC asara a Edo.

Lekan Ojo ya bayyana haka ne a lokacin da ya yi hira da jaridar Vanguard bayan ‘dan takarar APC, Osagie Ize-Iyamu ya sha kashi a hannun jam’iyyar PDP.

KU KARANTA: APC ta na zargin wani Gwamna da marawa PDP baya a zaben Jihar Edo

Jigon na APC ya zargi tsohon gwamnan jihar Legas da kuma tsohon gwamnan Edo Adams Oshiomhole da cusa kansu a inda babu dalilin su shiga.

‘Dan siyasar ya ce tsofaffin gwamnonin kasar sun tsoma baki ya yi yawa yayin da ake daf da zaben.

A ra’ayinsa, wadannan manyan ‘yan siyasa sun kawowa Ize-Iyamu da jam’iyyar APC ‘dan-gashi a zaben gwamnan, a dalilin haka PDP ta samu damar cin zabe.

“Na san Ize-Iyamu ‘dan siyasa ne na gidi a jihar Edo, amma tsoma bakin Oshiomhole ya jawo masa gagarumar cikas.” Inji Mista Jackson Lekan Ojo.

KU KARANTA: Fayose ya yi wa Obaseki huduba game da barin PDP bayan zabe

Lekan Ojo ya daurawa Tinubu da Oshiomhole laifin shan kashi a hanun PDP
Ojo ya na ganin Tinubu ya jawowa APC asara
Source: Facebook

Ya ce: “Mutane su fahimci cewa gungun mutanen da su ka tsige Oshiomhole daga kan kujerar shugaban jam’iyyar APC su na nan sarai har yanzu.”

Ojo ya karkare da cewa, “Abin da tsohon gwamnan Legas, Asiwaju Bola Tinubu ya yi, sharri ya jawowa ‘dan takarar jam’iyyar APC ba alheri ba.”

A baya mun kawo maku dalilan da su ka sa APC ta ji kunya a zaben Gwamnan Edo. Daga ciki har da kiran da Bola Tinubu ya fito ya yi na cewa a zabi APC.

Bayan haka, ana zargin Adams Oshiomhole da rike wuka da naman jam’iyyar APC a jihar Edo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel