Tsohon bidiyon Shehu Idris ya na magana da Sarkin Kano kan Marigayi Ado Bayero

Tsohon bidiyon Shehu Idris ya na magana da Sarkin Kano kan Marigayi Ado Bayero

- A Ranar 20 ga watan Satumban 2020, Sarkin Zazzau, Shehu Idris ya rasu

- Kwanan baya sabon Sarki Aminu Ado Bayero ya kai wa Shehu Idris ziyara

- Marigayin ya na cikin manyan aminan tsohon Sarkin Kano Ado Bayero

Mun samu bidiyon wata haduwar kwanan nan ta marigayi mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris da Sarki Aminu Ado Bayero na kasar Kano.

An dauki wannan bidiyo ne a lokacin da sabon Sarkin Kano ya kai wa aminin mahaifin na sa, Shehu Idris, ziyara ta musamman bayan hawa kan mulki.

Sarkin Zazzau, Shehu Idris ya bayyana cewa ya na cikin manyan na kusa da Ado Bayero watau mahaifin Sarki mai-ci yanzu, wanda ya rasu a shekarar 2014.

KU KARANTA: 'Ya 'yan Sarkin da ake yi wa hangen samun sarautar kasar Zazzau

Sarki Shehu Idris ya fara jawabi ne da yi wa takwaransa, Aminu Ado Bayero da majalisarsa godiyan kawo masa wannan ziyara domin kara zumunci.

Shafin Masarautar KANO a Twitter, @HrhBayero su ka wallafa wannan bidiyo a ranar Litinin.

A wannan bidiyo, Marigayin ya bada labarin yadda su ke haduwa bini-bini da Ado Bayero, ya ce su kan hadu ne a marabar Kano da Zariya a garin Faki.

Marigayi Shehu Idris ya ce a ganawarsa ta karshe da Ado Bayero bayan ya dawo daga kasar Ingila, Ado ya fada masa wata magana mai sosa zuciya.

KU KARANTA: Gwamnonin da su ka yi zamani da Sarkin Zazzau a Jihar Kaduna

Tsohon bidiyon Shehu Idris ya na magana da Sarkin Kano kan Marigayi Ado Bayero
Marigayi Shehu Idris
Source: Facebook

Sarkin Kano Ado Bayero wanda ya yi shekaru sama da 50 a gadon mulki ya shaidawa Shehu Idris cewa duk Duniya shi kadai ya rage masa a wancan lokaci.

Mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero ya cigaba da zumuncin da mahaifinsa ya mutu a kai bayan ya dare mulkin gidan dabo a watan Maris din shekarar nan.

A karshen makon jiya ne shi ma Mai martaba Shehu Idris ya cika, ya na da shekara 84 a Duniya. Mai martaba ya shafe shekaru 45 ya na kan mulkin Zazzau.

Shi ma Marigayi Ado Bayero ya rasu ne ya na da kusan shekaru 84 da haihuwa a shekarar 2014.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel