Kabilar Jarawa: Jama'ar kasar India da masana'antar Bollywood bata bayyanawa

Kabilar Jarawa: Jama'ar kasar India da masana'antar Bollywood bata bayyanawa

- Akwai wasu mutane a Indiya da ba lallai ne duniya ta taba jin labarinsu ba kuma ana kiransu da Jarawa

- Sun kasance kabila a kasar kuma a yanzu haka yawansu ya kai tsakanin mutane 250 da 400

- Yan kabilar Jarawa sun kasance bakaken fata kuma suna zama ne a tsibirin Kudancin Andaman da Tsakiyar Andaman

Ba lallai ne ace Bollywood ta nuna maku yan kabilar Jarawa ba, amma suma yan asalin kasar Indiya ne kuma sun kai kimanin mutane 250 zuwa 400.

A bisa ga shafin Wikipedia, mutanen wannan kabila na zama ne tsibirin Kudancin Andaman da Tsakiyar Andaman.

Legit.ng ta tattaro cewa yan kabilar Jarawa sun yi nasarar rike al’adunsu saboda yin watsi da hulda a tsakaninsu da yan waje a cikin shekarun 1990s.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya karbi bakuncin Buni da Ganduje a Aso Rock

Kabilar Jarawa: Jama'ar kasar India da masana'antar Bollywood bata bayyanawa
Kabilar Jarawa: Jama'ar kasar India da masana'antar Bollywood bata bayyanawa Hoto: Survival International
Asali: UGC

A shekarun 1990s, hulda tsakanin wannan kabila da jama’a ya karu kuma a shekarun 2000s, yan Jarawa sun zamo baki wuraren zaman jama’a.

Suna mu’amala da masu zuwa yawon bude ido, suna samun taimako na kiwon lafiya sannan harma suna tura yaransu makaranta.

Yan kabilar Jarawa sun mamaye tsibirin tsawon dubban shekaru masu yawa.

KU KARANTA KUMA: Nasarar PDP a zaben Edo: Okorocha ya yi wa APC wankin babban bargo

A gefe guda, wani bincike da aka yi ya nuna cewa masu amfani da harshen Hausa na cikin wadanda su ka fi yawa a Duniya.

Duk Afrika dama dai yanzu babu yaren da yayi fice irin na Hausa. Ana amfani da yaren a kasashen Nahiyar barkatai. Harshen Hausa shi ne mafi karbuwa a cikin Nahiyar Afrika

Akwai sama da mutane miliyan 150 da ke Hausa

Spectator Index ta bayyana cewa wani nazari da aka yi ya nuna cewa sama da mutane miliyan 150 ke amfani da harshen na Hausa.

Yaren dai shi ne na 11 cikin sahun wadanda su kayi fice a Duniya. Hausa na bayan irin su harshen Mandarin ne da Hindu.

Haka zalika an tabbatar da cewa akwai masu amfani da harshen Kasar Sifen da kuma Larabci da yaren kasar Rasha da duk sun sha gaban Hausa.

Akwai kuma irin su Yaren Malay da Bengali na Yankin Asiya wanda su na gaban yaren na Hausa.

Hausa dai na bin bayan yaren Kasar Foshugal ne da kuma Faransanci.

Amma masu yaren Hausa a Duniya sun kere yawan Jamusawa da mutanen Fashiya da kuma masu amfani da yaren Swahili na gida.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel