Yanzu Yanzu: Buhari ya karbi bakuncin Buni da Ganduje a Aso Rock

Yanzu Yanzu: Buhari ya karbi bakuncin Buni da Ganduje a Aso Rock

- Shugaban rikon kwarya na APC, Mai Mala Buni da Gwamna Ganduje sun gana da shugaba Buhari a Aso Rock

- Gwamna Obaseki ya kayar da dan takarar APC, Osagie Ize-Iyamu a zaben gwamnan Edo da aka yi a ranar Asabar

- Ziyarar gwamnonin na iya samun nasaba da sakamakon zaben

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Litinin, 21 ga watan Satumba, ya karbi bakuncin shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Mai Mala Buni.

Buni ya ziyarci shugaban kasar ne tare da Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

KU KARANTA KUMA: Makusanta shugaban kasa su na amfani da biyan tallafin man fetur don azurta kansu - Shugaban NNPC

Koda dai shugaban kasar ya gana da gwamnonin ne cikin sirri sannan jiga-jigan na APC basu yi jawabi ga manema labarai ba, ana zaton sun gana ne kan sakamakon zaben gwamnan Edo.

Yanzu Yanzu: Buhari ya karbi bakuncin Buni da Ganduje a Aso Rock
Yanzu Yanzu: Buhari ya karbi bakuncin Buni da Ganduje a Aso Rock Hoto: Ganduje
Source: Facebook

A ranar Asabar, 20 ga watan Satumba ne aka yi zaben.

KU KARANTA KUMA: Yadda masarautar Zazzau ke zaben sabon Sarki

Dan takarar jam’iyyar APC a zaben, Fasto Osagie Ize-Iyamu ya sha kaye a hannun dan takarar Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Godwin Obaseki.

A wani labarin, Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari bai taba yin amfani da isarsa ba ta yadda bai dace ba.

El-Rufai ya sanar da hakan a ranar Litinin yayin tsokaci a kan zaben gwamnan jihar Edo da aka yi a ranar Asabar da ta gabata, The Cbale ta tabbatar.

Godwin Obaseki, dan takarar jam'iyyar PDP a zaben, ya kada Ize-Iyamu na jam'iyyar APC da tazara mai yawa.

A yayin jawabinsa a shirin Sunrise Daily, wani shiri na gidan talabijin na Channels, El-Rufai ya ce yana fatan APC za ta ci zaben.

Kamar yadda yace, alamu sun nuna cewa jam'iyya mai mulki ce za ta yi nasara har sai a makonni uku da suka gabata.

Ya ce, "Ba kamar sauran gwamnatoci da suka gabata ba, Buhari yana bari a bar zabin jama'a a yayin zabe.

"Mun so yin nasara. A gaskiya ina ta mana fatan nasara tare da sa rai har sai da makonni uku da suka gabata. A nan alamun faduwarmu ta bayyana."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel