Okorocha ya caccaki APC bayan PDP da Obaseki sun lashe zabe a Edo

Okorocha ya caccaki APC bayan PDP da Obaseki sun lashe zabe a Edo

- Tsohon gwamnan jihar Imo, Okorocha, ya ce APC ta kare, cewa abunda ya rage kawai shine mutuncin Buhari da ake gani

- Sanatan na Imo ta yamma ya yi wannan furuci ne biyo bayan mummunan kaye da jam’iyyar ta sha a zaben gwamnan Edo da aka kammala

- Okorocha ya daura alhakin rikicin da jam’iyyar kefama dashi kan jiga-jiganta

Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya yi magana kan rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, biyo bayan kaye da ta sha a zaben gwamnan Edo.

Okorocha, sanata mai wakiltan yankin Imo ta yamma, ya ce APC ta kare, cewa abunda ya rage ma jam’iyyar shine mutuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ake gani.

Tsohon gwamnan wanda ya kasance jigon APC ya daura alhakin rikicin da ke addabar jam’iyyar kan ayyukan wasu jiga-jiganta.

A cewarsa, bai cire kowa ba a iyayen jam’iyyar illa Shugaban kasa Buhari.

Okorocha ya caccaki APC bayan PDP da Obaseki sun lashe zabe a Edo
Okorocha ya caccaki APC bayan PDP da Obaseki sun lashe zabe a Edo Hoto: Fadar shugaban kasa
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Al’umma sun yi babban rashi – Sheikh Gumi ya yi martani kan mutuwar Sarkin Zazzau

Daily Trust ta ruwaito cewa Okorocha ya fadi hakan ne a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba, lokacin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja.

Ya kuma ce jam’iyyar ta watsar da manufofin ci gaba da damokradiyya wanda akan ta ne aka kafa ta.

Yanzu iyayen jam’iyyar sun zama sune a baya sannan mutane na zuwa da ra’ayoyinsu mabanbanta suna sa mu yin irin siyasar PDP,” in ji Okorocha.

Okorocha ya ce jam’iyyar ba za ta ga daidai ba har sai Shugabannin ta sun koma inda duk suka fara.

APC ta kare, abunda muka rage dashi shine ganin mutuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari, wannan ne ke ajiyemu a tare. Mutuncin Shugaba Buhari kawai muke gani yasa muke ganin za a iya yin wani abu.

KU KARANTA KUMA: Hotunan yadda dandazon jama'a suka cika wajen jana'izar Sarkin Zazzau

Wannan yardar da ganin mutunci ne muke kira APC har yanzu, mutuncin shugaba Buhari da aminci da yardar cewa yana iya tashi wata rana sannan ya gyara duk wani rashin adalci. Wannan ne kadai yake tsare APC, idan ba don haka ba, bana tunanin akwai wata aba mai kama da APC saboda mutane sun fara gajiya. Kuma, ba wai PDP ta fi bane, jam’iyyar na da nata matsalolin,” in ji sanatan na APC.

A gefe guda, mun kawo maku cewa a zaben jihar Edo, ‘dan takarar PDP, Godwin Obaseki ya doke Osagie Ize-Iyamu na jam’iyyar APC mai hamayya a kananan hukumomi 13 a cikin 18 da ke jihar.

APC ta yi nasara ne kurum a yankin Owan da Etsako. Ita kuwa PDP ta yi galaba a Igueben, Ikpoba-Okha, Uhunmwonde, Yankunan Esan, Egor, Owan, Ovia, Oredo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel