Hadimin shugaban kasa Bashir Ahmad na shirin angwancewa da amaryarsa Naeema (hoto)

Hadimin shugaban kasa Bashir Ahmad na shirin angwancewa da amaryarsa Naeema (hoto)

- Hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad na shirin angwancewa

- Za a daura auren Bashir da amaryarsa Naeema Junaid a babban masalin Juma’a da ke GRA, Katsina a ranar 25 ga watan Satumba

- Bashir da kansa ne ya bayar da wannan sanarwar a shafinsa na Twitter

Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari na musamman a shafukan zumunta, na shirin angwancewa da masoyiyarsa.

Hadimin shugaban kasar zai auri amaryarsa, Naeemah Junaid a ranar Juma’a, 25 ga watan Satumba.

Za a daura auren ne babban masallacin Juma’a na GRA da ke Katsina.

Hadimin shugaban kasa Bashir Ahmad na shirin angwamcewa da amaryarsa Naeema (hoto)
Hadimin shugaban kasa Bashir Ahmad na shirin angwamcewa da amaryarsa Naeema Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Kai tsaye: Yadda zabe gwamnan jihar Edo tsakanin Obaseki da Ize-iyamu ke gudana

Da yake sanar da batun auren nasa a shafin Twitter, Bashir ya wallafa:

Lokacin da aka dade ana jira ya zo!

"@Naeeemah_x da ni muna gayyatarku zuwa wajen daurin aurenmu a ranar 25 ga watan Satumba, 20202 a babban masallacin Juma’a na GRA, Katsina.

"Lokaci: Karfe 2:00 na rana. Idan baku samu zuwa ba saboda kowani dalili, ku saka mu a cikin addu’o’inku. Nagode. #NB2020.”

A wani labarin kuma, yan Najeriya da dama sun caccaki iyalan shugaban kasa a kan karya dokar babban bankin Najeriya (CBN) a wajen bikin Hanan Buhari, daya daga cikin yaran shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Mutane da dama sun kuma yi wasti da take dokar bayar da tazara a tsakanin jama’a wanda hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta bayar don hana yaduwar cutar Coronavirus.

Hanan da Turad, dan tsohon dan majalisar dokokin tarayya, Mahmud Sani Sha’aban, sun yi aure a fadar shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Kano: Yan sanda sun kama matar da ta kashe dan kishiyarta

Bikin ya samu manyan jami’an gwamnati da yan siyasa.

Hotuna da bidiyon bikin ciki harda wanda uwargidar shugaban kasar, Aisha Buhari ta wallafa a shafinta na Instagram sun yi fice a karshen makon.

A wani bidiyo da Sahara Reporters ta wallafa, an gano ma’auratan na rawa tare wadanda suka halarci bikin inda aka yi ta lika kudi.

An taru waje daya ba tare da barin tazara ba a cikin bidiyon sannan mafi yawan mutanen da ke wajen basu sanya takunkumin fuska ba.

Wannan ya haifar da cecekuce yayinda mutane da dama suka nuna rashin jin dadinsu a kan yadda manyan mutane da sauran da suka hallara suka take dokokin CBN da na NCDC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng